Ministan Yada Labarai Lai Mohammed ya shaida wa Majalisar Dattawa cewa Gwamnatin Tarayya na neman hadin kan Majalisa domin a fito da dokokin da za su taka wa soshiyal midiya burki daga watsa labarai na karairayi da bayanan bogi.
Lai ya yi wannan bayani a ranar Laraba a Majalisa, lokacin da ya ke kare kasafin kudi na 2021 na ma’aikatar sa.
Da ya ke bayani a gaban Kwamitin Harkokin Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Minista ya ce masu kirkirar karairayi da bayanan bogi a soshiyal midiya, su ne sahun gaba na kawo wa kasar nan barazana.
Lai ya yi wannan bayani ne a matsayin amsar wata tambaya da ‘yan kwamitin su ka yi masa, dangane da abin da su ka ce yadda soshiyal midiya ta ruruta zanga-zangar #EndSARS zuwa tarzoma da kuma yadda gwamnati za ta magance lamarin nan gaba.
Lai ya ce soshiyal midiya ta zame wa masu kirkirar karairayi wani dandalin baza ji-ta-ji-ta da labarai na bogi da na tayar da husuma.
Dalili kenan Ministan ya ce akwai matukar bukata gwamnatin Najeriya ta kakaba wa soshiyal midiya takunkumi da dabaibayin haka baza karairayi da bayanan bogi.
Don haka ya ce akwai bukatar kirkiro hanyoyin sadarwa na zamani masu karfin dakile soshiyal midiya a kasar nan.
Kokarin Kulle Google, Facebook Da Instagram A Najeriya:
“Idan ka je Chana za ka samu babu Google, babu Facebook kuma babu Instagram. Sai e-mel kadai su ke da shi, amma sun kulle sauran daga aiki a kasar.
“A Ethiopia an yi kisan wani mawaki. Amma da gwamnatin kasar ta ga soshiyal midiya na neman hargitsewar kasar, sai ta rufe dukkan kafofin sadarwa a kasar tsawon kwana biyu. Kuma lokacin ana cikin taron Shugabannin Kasashen Afrika.” Inji Lai.
Shugaban Kwamiti Olusegun Odebunmi, ya kara sharhi da bayani a kan kalamai da misalan Lai. Ya ce an watsa bidiyon bogi wajen nuna cewa wai sojoji sun bude wa masu zanga-zanga wuta a Lekki, kuma hakan ya haddasa bala’i a kasar nan.
“Lokacin zanga-zanga a Lekki, na ga an nuno wani soja rike da bindiga samfurin mashinga, ya na bude wa masu zanga-zanga wuta a Lekki. Yadda ya ke bude wuta, kai sai ka rantse ka ce a fagen yaki ya ke
“To amma daga baya, sai ta tabbata cewa hada bidiyon aka yi, wato photoshop.”
Sauran ‘yan kwamiti sun nuna muhimmancin soshiyal midiya wajen kawo sauyin ci gaban al’amurra a saukake. Amma kuma duk da haka, sun ce akwai bukatar yi mata takunkumi da dabaibayi.