Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto ya karyata zargin da ake yi masa cewa gwamnatin sa ta boye kayan tallafin rage radadin korona, ya ki rabawa a jihar sa.
Gwamna Aminu Tambuwal ya yi wannan ikirarin a lokacin da ya ke wa jama’a jawabi dangane da kokarin sa ba ganin an yayyafa wa wutar rikicin da ta tirnike kasar nan, sanadiyyar zanga-zangar #EndSARS.
Ya ce zanga-zangar ta rikide zuwa tarzoma, inda jama’a su ka rika fasa sito daban daban domin kwasar kayan tallafin korona.
“Babu wani dalilin da zai sa jihar Sokoto ta boye kayan tallafi ta hana mutane.
” Dalili kenan ba a samu rahoton tashin hankali ko hayaniyar fasa wasu sito ko rumbunan ajiyar abinci ba.
Tambuwal ya ce jihar Sokoto ta karbi kayan tallafi sau biyu, tun bayan barkewar cutar korona a kasar nan.
“Mun karbi kayan tallafi daga CACOVID, wadanda tallafi ne daga gamayyar ‘yan kasuwa da kuma kamfanoni.”
Ya ce wadanda su ka bada tallafin ne su ka nemi a dan jinkirta. Kuma daga lokacin da aka cewa gaba, an raba kayayyakin a karkashin sai-idon Sakataren Gwamnatin Jiha, Sa’idu Umar.
Sai kuma kayan tallafin da aka karba ranar 17 Ga Oktoba, na Gwamnatin Tarayya ta hannun ofishin Ministar Harkokin Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa, Sadiya Farouq.
“Shi kuma wannan Minista ce da kan ta ta ce a yi mata alfarma, a jira ta zo a yi rabon a gaban ta. Wannan shi ne dalilin da ya sa ku ka ga mu na kan aikin raba tallafin a yanzu.” Inji Tambuwal.
Baya ga Gwamna, Ministan Harkokin ‘Yan Sanda Maigari Dingyadi da Sultan Abubakar III, duk sun ja hankulan matasa a guji tayar da hankula.
Sun kuma yabi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari dangane da kokarin da ta ke yi wajen inganta rayuwar marasa galihu.