Fannin kiwon lafiyar Najeriya na fama da matsaloli na rashin samun kula daga gwamnati wanda yasa ake fama da matsaloli masu yawan gaske da har yanzu kasa Najeriya ke fama da su.
Rashin ware wa fannin isassun kudade, rashin isassu da kwararrun ma’aikata, yawan yajin aiki, rashin isassun asibitoci, karancin magunguna da dai sauran su na daga cikin matsalolin da suka gurguntar da fannin kiwon lafiyar kasar nan.
A dalilin haka mata da yara kananan sun fi fadawa cikin wannan matsala wanda har rayukansu ake rasawa.
Mutane dai suke ji a jika, domin ya kai ga a wannan kasa mata na tara ƴan kuɗaɗen su, taro sisi su sai motar da zai rika yi musu jigilar marasa lafiya saboda gazawar gwamnati.
Bayan haka kuma, akwai matsalar karancin adibitocin da kuma yadda magunguna karya suka karade kasuwannin kasar nan.
Mutane da dama sun fada cikin matsanancin rashin lafiya a dalilin sakacin likitoci a asibitoci da kuma shaye shayen maganin da ba na kwarai ba.
Najeriya na da aiki a gaba musamman a fannin kiwon lafiya na kasar, idan har tana so a iya shawo kan matsalolin da yayi mata rawani a ka.
1. Tarin fuka
Tarin fuka cuta ce dake kama huhu davake shakar kwayoyin cutar daga iska.
Likitoci sun ce cutar na yaduwa nan-da-nan idan ana yawan cudanya da masu fama da cutar domin mutum daya dake dauke da cutar na iya yada wa mutane 15 a cikin dan kankanin lokaci.
Najeriya na daya daga cikin kasashe 30 da wannan cuta ta yi tsanani a cikinta kuma itace kasa ta farko da cutar ta fi yawa a cikinta a Nahiyar Afrika.
Duk shekara mutum 245,000 na rasa rayukansu a dalilin kamuwa da cutar a Najeriya baya ga mutum 590,000 dake kamuwa duk shekara.
An kuma gano cewa mutum 14,000 daga ciki masu fama da cutar suna dauke da Kanjamau.
2. Ciwon siga
Ciwon siga na kama mutum ne idan aka samu matsala da wasu daga cikin ababen da ke sarrafa abincin da ake ci a cikin mu.
Sakamakon binciken majalisar dinkin duniya ya nuna cewa cutar ta yi ajalin mutane miliyan 1.6 a duniya.
Majalisar ta ce domin rage yaduwar wannan cuta za ta yi amfani da watan Nuwanba ta kowace shekara domin wayar da kan mutane ilolli da hanyoyin guje wa kamuwa da cutar tare da rage tsadan farashin magunguna domin mutane su iya siyan maganin.
A Najeriya, ciwon Siga yana yi wa mutane da dama illa. Rashin sani da wayar wa mutane kai game da yadda za su kiyaye da kare kansu na daga cikin abubuwan da ke sa cutar na yi wa mutane lahani matuka.
3. Zazzabin lassa
Zazzabin Lassa cuta ce da ake kamuwa da ita a dalilin cudanyar bera da abincin da muke ci. Wannan cuta dai a sannu a hankali tana ta afkawa mutanen kasar nan.
Ya kan yi wahala a gano cutar a jikin mutum domin ya kan dauki tsawon kwanaki shida zuwa 21 kafin ta bayyana a jikin mutum.
Duk shekara cutar sai ta bullo a kasar nan a dalilin rashin gano maganinta sannan da rashin wayar da kan mutane game da cutar da hanyoyin samun kariya daga kamuwa da cutar da gwamnati ba yi yadda ya kamata. Jihohi irin su Bauchi, musamman a Arewacin Najeriya ne suka fi fama da wannan cuta ta Zazzabin Lassa.
4. Nimoniya
Ciwon sanyi dake kama hakarkari ‘Pneumonia’ cuta ce na sanyi dake kama hakarkarin mutum a dalilin shakan gurbataccen iska da kuma yawan amfani da kayan sanyi.
Cutar na daya daga cikin cututtuka biyar dake kisan yara kanana ‘yan kasa da shekaru biyar a duniya.
Sakamakon binciken da jami’ar ‘John Hopkins’ ta yi ya nuna cewa nan da shekaru 10 masu zuwa Najeriya za ta iya rasa yara ƴan kasa da shekaru biyar akalla miliyan biyu a dalilin kamuwa da cutar sanyi ‘Nimoniya’.
Kwayoyin cuta na ‘Virus, Bacteria da Fungi’ ne ke haddasa wannan cuta.
Inganta kiwon lafiyar yara kanana musamman a bangaren allurar rigakafi, shayar da jarirai nono, ciyar da yara abincin da zai gina musu garkuwan jiki na daga cikin hanyoyin da zai taimaka wajen ceto rayukan akalla yara 809,000 a kasar nan.
5. Dajin dake kama nono
Ciwon dajin da ke kama nono na kama nonon maza da mata kuma yana daya daga cikin cututtukan da ke kashe mutane a kasa Najeriya.
Dajin da ke kama nono shine mafi saukin ganewa domin cutar na nuna alamu kamarsu kunburin nono,fatar nonon ya canja kala, nono zai rika fitar da ruwa da kuma sauransu.
Mata musamman na Karkara na fama da wannan ciwo a Najeriya. Karancin wuraren kula da masu fama da ciwon da magani na daga cikin matsalolin da ake fama da su a Najeriya.
6. Ciwon Yoyon fitsari
Najeriya na cikin jerin kasashen duniya da ciwon yoyon fitsari ya yi tsanani domin sakamakon bincike ya nuna cewa mata 400,000 zuwa 800,000 na fama da wannan matsala a kasar nan.
7. Dajin dake kama ‘ya’yan maraina.
Bincike ya nuna cewa wannan cutar na daya daga cikin cututtukan dake yawan kisan maza a duniya.
Alamun wannan cutar sun hada da rashin iya yin fitsari yadda ya kamata,yin fitsari da jini,ciwon kirji da sauran su.
Likitoci sun bayyana cewa shan taba,shan giya na kawo cutar sannan ma aka iya gaji cutar.
Maza da dama a Najeriya na fama da wannan cuta. Rashin Sani da wayar musu da kai shine yayi karanci.
8. Zazzabin cizon sauro
Sakamakon binciken da kungiyar kiwon lafiya ta duniya ta gudanar a shekarar 2018 ya nuna cewa Najeriya na da kashi 25 cikin kason adadin yawan mutanen dake dauke da zazzabin cizon sauro a duniya.
Rashin tsaftaci muhalli, magudanar ruwa da kuma rashin maida hankali da gwamnati bata yi ba wajen bunkasa asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya musamman a karkara suna daga cikin abubuwan da ake fama da su
9. Kanjamau
Cutar kanjamau cuta ne dake karya garkuwar jikin mutum.
Har yanzu dai babu maganin warkar da cutar amma masana kimiya sun hana maganin da ke da inganin hana yaduwar cutar a jikin mutum da ake bai wa masu fama da cutar kyauta.
Karancin maganin cutar, rashin yin gwajin cutar,rashin wayar da kan mutane game da cutar na daga cikin matsalolin dake kawo wa Najeriya cikas wajen yaki da cutar.
Hukumar hana yaduwar cutar kanjamau ta kasa NACA ta gabatar da sakamakon binciken adadin yawan mutanen dake dauke da kanjamau a Najeriya.
Sakamakon ya nuna cewa mutane miliyan 1.9 ne ke dauke da cutar kuma matasa masu shekaru 15 zuwa 49 ne suka fi yawan wadanda suka kamuwa da cutar.
10. Korona Bairos.
Ita wannan sabuwar cuta ta Korona, ba Najeriya, duk Duniya ake ta fama da ita.
Har yanzu ba a samu maganinta ba sai dai ana mata ƴan dabaru idan mutum ya kamu har ya warke.
A Najeriya sama da mutum 50,000 sun kamu da cutar, sama da 1000 sun rasu.