Ƙungiyar ƴan Najeriya Masu Kasuwanci a Ghana (NUTAG), ta gudanar da zanga-zangar lumana ga gwamnatin kasar, sakamakon kin bude masu shaguna da ‘yan Najeriya ke hada-hada, da gwamnatin Ghana ta yi tsawon lokaci.
Shugaban Kungiyar ‘Yan Kasuwa Mazauna Ghana ‘Yan Najeriya, Chukwuemeka Nnaji, ya yi bayani cewa shi ne ma ya ja zugar zanga-zangar, saboda tun da 2020 ta shigo, ba a bari sun bude kantinan su ba.
Ya ce rabon da su bude shaguna si yi hada-hada, tun cikin 2019.
Nnaji ya ce gwamnatin Ghana ta ki bude masu shaguna duk kuwa yawan zaman cimma yarjejeniyar fahimtar juna da aka kulla tsakanin gwamnatin Najeriya da ta Ghana.
Ya ce sun gudanar da zanga-zangar ce domin gwamnatin Ghana ta bude masu shaguna su ci gaba da kasuwanci, yadda za su farfado daga halin kuncin da su ka shiga sanadiyyar bsrkewar cutar korona a duniya.
Daga nan kuma ya yi kira ga gwamnatin Najeriya ta dawo da ‘yan Najeriya da ke son dawowa gida daga Ghana zuwa gida.
Nnaji ya ce ya yi magana da Shugaban Kungiyar ‘Yan Tiredar Najeriya, Ken Okoha, kuma ya yi alkawarin zai gaggauta sanar da halin da su ke ciki yanzu haka ga Ghana ga mahukuntan Najeriya.
Sai dai kuma ya tabbatar da cewa har yanzu akwai cutar korona a Ghana, kuma ya shawarci ‘yan Najeriya masu kasuwanci a Ghana su xi gaba da zama gida, idan ba su da wani sahihin abu da za su fita su yi a waje.
“Ina tabbatar maku idan nan da karshen Oktoba ba a yi komai a kan halin da mu ke ciki ba, to za mu dawo gida.” Inji Nnaji.
Jami’ar Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Ghana, Easter Arewa, ta karbi masu zanga-zangar, kuma ta yi masu alkawarin gaggauta duba matsalar su.