Ƴan takife sun fatattaki sarki, sun kulle fadar sa da makulli

0

A ranar Litinin ce hasalallun matasan da ba su jin maganar kowa su ka fatattaki basarake Oba Olatunde Falabi, Akire na Ikire a Jihar Osun.

An tabbatar da sun kore shi, bayan ya arce kuma sun da makulli sun kulle fadar ta sa.

Sojoji ne su ka cece shi daga hannun matasan wadanda dama kacokan sun je domin su fitar da shi daga fadar da karfin tsiya.

Matasan sun kore shi ne saboda gwamnatin Osun ta ki yin amfani da hukuncin da Kotun Koli ta zartas cewa nadin da aka yi wa sarkin haramtacce ne.

Kakakin ƴan Sanda na Jihar Osun, Opalola Yemisi ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce ba a rasa rayuka a tarzomar ba.

Rikicin nadin da dai ya samo asali ne tun 1987, bayan mutuwar tsohon Sarki Oba Oseni Oyegunle.

Lokacin da batun nadin sabon sarki ya taso, sai daya daga cikin gidaje biyar masu hakkin cancanta yin sarauta a masarautar, su ka fitar da dan takarar su Tajudeen Olanrewaju, wato Gidan sarauta na Aketula kenan, kamar yadda dokar nadin sarkin Akire na Ikire ta tanadar tun daga 1958.

Sai dai kuma tun kafin nadin, sai gidajen sarauta biyu su ka garzaya kotu, su ka kalubalanci saka gidan Aketula cikin jerin masu neman sarauta.

Hakan ne ta sa Babbar Kotun Osun a Ile Ife ta hana a nada Olanrewaju sarauta. Daga nan ne aka nada Oba Olutunde Falabi a cikin 1993. Shi ma aka yi ta markabun shari’a har zuwa Kotun Koli.

Kotun Koli ta haramta sarautar sa tun a 2014.

Share.

game da Author