Ƴan sara-suka sun mamaye ofishin ƴan sanda, sansanin kwastan da ofishin jami’an NSCDC a Oyo

0

Wasu fusatattun matasa sun kai hari ofishin ƴan sanda, su ka afka sansanin jami’an kwastan sannan su ka kai farmaki a ofishin jami’an NSCDC a jihar Oyo.

Ofishin ƴan sandan da su ka kai wa harin ya na garin Iseyin da ke yankin Oke-Ogun.

Matasan wadanda su ka ce su na zanga-zanga ne a kan damuwar su kan yadda ƴan sanda ke gallaza masu, sun zarce kuma inda su ka mamaye mamaye sansanin jami’an kwastan da ke garin da kuma ofishin jami’an tsaro na NSCDC.

Sun kai farmakin ne daidai lokacin da zanga-zangar #EndSARS ta shiga sati biyu cur a fadin kasar nan.

Wakilin mu ya gano cewa masu zanga-zangar sun danna cikin ofishin ƴan sanda, su ka kwashe kayayyakin da ke ciki.

Sun kuma danna cikin ofishin kwastan, su ka jide shinkafa da sauran kayan masarufin da kwastan su ka kama daga hannun masu fasa-kwauri.

A ofishin NSCDC ma sun danna kan su tsaye kuma su ka saci kayayyaki masu yawa.

Bidiyon da PREMIUM TIMES ta samu ya bayyana yadda masu zanga-zanga su ka rika jidar kayayyaki a ofishin ƴan sanda, har da janareto da kuma Talbijin.

Shugaban Riko na Karamar Hukumar Iseyin, Mufitau Abilawon, ya tabbatar da afukuwar lamarin a ranar Alhamis da rana.

Ya a ranar Laraba an tattauna batun yadda za a zauna lafiya a garin, har aka amince matasa su taru kofar fadar basaraken Iseyin, Aseyin Abdulganiy.

Sai dai kuma hakan bai yiwu ba, sai su ka wayi gari da tarzoma.

PREMIUM TIMES ta nemi jin ta bakin kakakin ‘yan sanda da sauran na jami’an tsaro. Amma ba a amsa kira ba.

Share.

game da Author