Ministan Ayyuka da da Gidaje Babatunde Fashola, ya ja hankalin ƴan Najeriya cewa su daina kallon Buhari ne zai magance kowace irin matsalar kasar nan, musamman matsalolin da jihohi ne su ka kamata su magance.
Ya ce ƴan Najeriya su na tsangwamar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ne saboda tunanin su gwamnatin sa ce za ta magance dukkan gagariman matsalolin da dokar kasa ta ce jihohi ne ke da alhakin magance su.
Ya ce dokar tsarin mulkin Najeriya bai dora wa gwamnatin tarayya wani nauyi mai yawan da ya kai na jihohi ba.
“Saboda jama’a sun yi zaune turus kowa na jiran Gwamnatin Tarayya ko Shugaban Kasa ya yi masu aiki, shi ya sa su ke ta tsangwamar gwamnatin. To ina faɗa maku mu na neman a yi mana ayyuka ne, ba a inda ya dace mu nemi a yi mana ba.”
Haka Fashola ya bayyana a tattaunawar sa da Gidan Talbijin na Channels a ranar Alhamis.
Daga nan sai Fashola ya yi ga daukacin ‘yan Najeriya cewa kowa ya je ya karanta Tsarin Dokokin Najeriya, domin ya ga yadda doka ta karkasa ayyukan gwamnatin tarayya, na jihohi da na kasanan hukumomi.
Ya ce idan su ka yi haka, to za su daina tunanin Buhari ne zai yi masu ayyukan da jiha ko karamar hukuma su ka cancanci yi masu ayyukan.
“Shi fa aikin gwamnatin ba wani siddabaru ba ne. Ya kamata jama’a su farga cewa yawancin abin da su ke sa rai gwamnatin tarayya za ta yi masu, ko akasarin su duk jihohi ne ko ma kananan hukumomi su ka kamata su samar wa jama’a su.
Cikin kadan daga ayyukan da Fashola ya ce kada ƴan Najeriya su sake tunanin Buhari ne zai samar musu, sun hada da samar da kiwon lafiya a matakin farko da ilmin firamare. Ya ce duk ba nauyin da ya rataya a kan Buhari ba ne. Hakkin jihohi ne.
Discussion about this post