Gungun ƴan daba dauke da sanduna, kokara, da karafuna sun tarwatsa dandazon masu zanga-zangar #EndSARS a Abuja ranar Laraba.
Matasan sun afkawa masu zanga-zanga ne inda suka farfasa motocin mutane sannan suka rika jibgan wadanda suka cigaba da zanga-zangar.
Anan dai aka yi arangama inda daga baya suka yi tafiyarsu.
Anji wa wasu biyu daga cikin ƴan daban rauni, wasu kuma da dama daga cikin masu zanga-zangan suma sun samu raunuka a jikin su.
Dukkan su dai an garzaya da su asibiti.
Duk da cewa gwamnati ta amince da bukatun da masu zanga-zangar suka bukata, har yanzu wasun su sun ki su janye daga titunan kasar nan musamman a jihohin kasar nan musamman jihohin Legas da Abuja da wasu kasashe jihohn kudancin kasar nan.