Tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Obadia Mailafia ya shaida wa jami’an SSS cewa zancen gaskiya ba shi da wata shaida ko hujjar da zai sa iya dogara don kare kan sa da ita, bayan subul-da-bakan kasassabar da ya yi cewa gwamnati ce ke da hannu wajen kashe-kashen da ake yi a kasar nan.
Ya kara da cewa sannan kuma ya shaida wa SSS a karo na ukun gayyatar da suka sake yi masa cewa ba shi da hujjar da zai iya bayarwa da ya yi ikirarin cewa akwai wani gwamna da ke saukar nauyin Boko Haram.
Mailafia ya yi wannan karin bayani bayan fitowa daga Ofishin SSS na Jos daga gayyatar da suka yi masa karo na uku.
“Sun karbe ni hannu bib-biyu, babu tirsasawa ko cin zarafi. Na yi musu gsmsasshen bayani cewa ba ni da hujjar wancan ikirari da na yi, domin ni ma ji-ta-ji-ta ce na dora.
“Kuma na fahimci kamata na yi na yi gwamnati hannun-ka-mai-sanda kan kashe-kashen da ake yi din. Ba wai na fito ina bobbotan da ba zan iya kawo hujja ko shaida kwakkwaara ba.” Inji Mailafia.
“Amma da a ce na tsaya na natsu kafin na yi maganar, da an fahimce ni sosai.”
Dangane da zargi da ya yi cewa ana yi wa rayuwar sa barazana, Mailafia ya ce to shi dai bai zargi kowa ba, domin babu wani da ya fito karara ya yi masa barazana gaba-da-gaba.
“Amma dai an yi ta kira na a waya, kuma kiran da ba a cika yi min ba. Akwai ma ranar da na ga bakon-ido su na kokarin kutsawa ta kyauren gida na. Ni kuma sai na tsallake katanga na gudu, saboda ban san ko su wane ba.”
Da ya ke magana kan zargin da ya yi cewa wasu manyan Najeriya na kokarin kashe shi, ya ce bai san ko su wa ne ba.
“Ni ma fada min aka yi. Ban san su ba. Idan ma na sani, ba lallai ba ne na sanar da ku.”
Ya ce ya na ganin kima da darajar jami’an SSS. Amma da wahala ya sake amsa gayyatar su zuwa Jos, domin rayuwar sa na cikin barazana, musamman ganin yadda ya ke bin hanya har Jos domin amsa gayyatar SSS.
Discussion about this post