Yaro ɗan shekara 13 da kotu ta yanke wa hukuncin ɗaurin shekaru 10 saboda ɓatanci ga Annabi (SAW) a Kano, ya ɗaukaka ƙara.
Wata Ƙungiyar Ƴancin Addini ce ta shigar da ƙarar a madadin sa, a Babbar Kotun Jihar Kano, a ranar Litinin.
A cikin karar da ƙungiyar mai suna ‘Foundation for Religious Freedom’ ta ɗaukaka a madadin yaron mai suna Umar Faruq, ƙungiyar ta maka Gwamna Abdullahi Ganduje da Antoni Janar na Jihar Kano Kano duk ta gurfanar a kotu.
Yayin da Mai Shari’a Aliyu Kani na Babbar Kotun Shari’a ta yanke wa Farouk daurin shekaru 10, shi kuwa Shariff Aminu hukuncin kisa ta hanyar rataya aka yanke masa a cikin watan Agusta.
Dukkan su dai an yanke musu hukunci saboda batanci da ake zargin sun yi wa Annabi (SAW), a ranar 10 ga Agusta.
An yanke wa su biyun hukunci ne a bisa Sashe na 382 na Dokar ‘Penal Code’ ta Jihar Kano ta 2000.
Ƙungiyar ta FRF dama kuma ta rigaya ta daukaka hukuncin da aka yanke wa Shariff na hukuncin ratayewa.
Gwamna Abdullahi Ganduje ya nuna cewa ba zai tsaya bata lokaci wajen sa hannu a rataye Shariff ba, matsawar duk wani sharuddan da kotu ta gindaya duk an cike su.
Daukaka Ƙara:
Ƙungiyar RFR ta bayyana garƙamewar da aka yi wa Farouk cewa an danne masa ‘yancin sa na Dan Adam wanda yarjejeniyar Afrika ta baiwa da Ƙundin Tsarin Dokokin Najeriya suka ba shi.
Sun ce wannan hukunci da aka yanke masu duk ba shi da wurin zama da Dokokin Tsarin Mulkin Najeriya, na 1999.
Ƙungiyar ta kara da cewa laifin sabo na addini ba laifi ba ne a karkashin Dokokin Najeriya.
Sun ce Dokar ‘Penal Code’ ko Shari’a ba su da murin zama a ƙarkashin Dokokin Najeriya.
Discussion about this post