A kokarin da Gwamnatin Tarayya ke yi domin ganin Kungiyoyin Kwadago na NLC da TUC ba su barke zanga-zanga a ranar Litinin da kuma zarcewa yajin aiki ba, za a yi wani taron gaggauwa tsakanin kungiyoyin da kuma Gwamnatin Tarayya.
Taron wanda za a yi ranar Lahadi a fara karfe 7 na yamma, za a shafe tsawon dare ana yamutsa gashin baki tsakanin bangarorin biyu.
Kungiyar Kwadago dai ta yanke shawarar tafiya yajin aiki da zanga-zanga ne bayan gwamnatin Buhari ta kara kudin fetur da kudi wutar lantarki.
Takura biyu da aka yi cikin makon da ya gabata domin ganin an shawo kan ‘yan kwadago bai yi nasara ba. Saboda sun ce sai gwamnati ta janye karin da ta yi sannan za ta janye yajin aiki.
Kokarin da Gwamnonin Najeriya su ka yi domin sasantawa ya ci tura.
An shirya yin taro tsakanin gwamnati da ‘yan kwadago a ranar Litinin, Amma saboda ganin sun ki janye yajin aikin aka maida taron baya zuwa yau Lahadi da karfe 7 na dare.
Kakakin Yada Labarai na Ma’aikatar Kwadago, Charles Akpan ne ya sanar da maido taron zuwa Lahadi.
Babbar Kotun Tarayya ta haramta zanga-zangar, sannan kuma ta umarci ‘yan sanda su tabbatar masu zanga-zanga ba su hana ma’aikatan gwamnati zuwa wurin aikin su ba.
Ita ma Shugabar Gwamnatin Tarayya ta fitar da gargadin cewa ma’aikatan gwamnatin tarayya su tabbatar sun fita aiki a ranar Litinin.
Kungiyar Kwadago dai ta ce babu gudu babu ja da baya, za ta tafi yajin aiki a ranar Litinin, bayan gama zanga-zanga a fadin kasar nan.