Ɗan takarar mataimakin gwamnan jihar Edo a inuwar jam’iyyar PDP ya yi barazanar kada da tsohon shugaban Jam’iyyar APC Adams Oshiomhole a mazaɓarsa a zaɓen gwamna dake tafe.
Philip Shu’aibu wanda shine Ɗan takarar mataimakin gwamnan jihar a inuwar Jam’iyyar PDP ya shaida cewa shine ya wayar wa Oshiomhole kai a harkar siyasar Edo kuma zai ɗanɗana kuɗarsa idan zabe ya zo.
” Shiyyar Edo ta Arewa tafi kowacce shiyya a wurin na sauƙin yin nasara domin kuwa tsarin siyasar wannan yanki na hannun mu ne. Saboda haka kamar mun ci mungama ne a wannan shiyya. PDP ce zata kwashe kuri’un wannan wuri Kaf.
” Ni ne na riƙe hannun Oshiomhole na tallata wa jama’a. Ni ne na shiga da shi sako-sako na nuna shi. Ni ne nake da jama’ar da yake takama dasu kuma zamu ragargaza shi a wannan zaɓe.
Shuaibu ya ce zai cigaba da mara wa gwamnan jihar Obaseki na jam’iyyar PDP baya don yayi nasara a zaɓen dake tafe.
Ranar 19 ga Satumba za a gudanar da zaɓen gwamna na jihar Edo. Da karfin tsiya jam’iyyar APC ta wancakalar da gwamna mai ci in ta zaɓi wani dabam dan takarar ta. A dalilin haka gwamna Obaseki ya canja sheƙa zuwa jam’iyyar PDP domin yin takara gwamnan jihar wanda ya ƙarato.
Discussion about this post