Dandazon ƴan jagaliyar siyasa daga ɓangaren Ƙungiyar Masu Sufurin Motocin Haya (NURTW), sun yi cincirindo a ƙofar harabar Majalisar Dokokin Jihar Ondo.
Dandazon ƴan-tashar dai sun kafa shinge tun da sanyin safiyar Litinin suka hana mambobin majalisa da ma’aikata shiga ciki, abin da ya haifar da rudani sosai.
Cincirindon dai an tabbatar da cewa Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Ondo, Bamidele Oleyologun ne ya gayyato su domin wata manufa ta siyasa.
An ce ya gayyato su ne domin su tada buyagi da hauragiya su hana wasu ƴan Majalisa su tara sake shiga majalisar.
Wadanda aka hana shiga din dai an dakatar da su ne run ranar 4 Ga Yuli, amma suka garzaya kotu ta soke dakatarwar da aka yi masu.
Dakatarwar dai na da nasaba da tsamin siyasa tsakanin Gwamna Rotimi Akeredolu da Mataimakin sa, Agbola Ajayi.
Dukkanin su biyu sun tsaya takarar zaben gwamnan Ondo, wanda za a yi cikin Oktoba, na watan gobe.
Sama da mako daya kenan da Babbar Kotun Akure ta bada umarnin su koma majalisa, amma magoya bayan kakakin majalasa sun hana su shiga ciki.
Ajayi ya samu sabani da Akeredolu, har ya fice daga APC ya koma PDP. Bayan an ki tsayar da shi takara s karkashin PDP kuma, sai ya tuma tsalle ya shiga ZLP, inda a can aka tsayar da shi takara.
Daga cikin wadanda aka hana shiga Majalisar a ranar Litinin, akwai Mataimakin Kakakin Majalisa, Iruju Ofun, Adewale William, Tomide Ajinribido da Favour Tomomowe.
Kakakin Yada Labaran ‘Yan Sanda na Jihar Ondo, Tee Leo ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa tuni jami’an su sun tarwatsa ‘yan buyagin, komai ya daidaita.
Ya ce tabbas Kakakin Majalisa ne ya gayyace su, amma bai san dalili ba.