ZABEN ONDO: INEC na neman gudummawar sarakunan jihar domin nasarar zabe

0

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta yi kira ga sarakunan gargajiya a Jihar Ondo da su taimaka wajen ganin masu zabe sun tabbatar da zaman lafiya da bin ka’idojin kare kai daga annobar korona a zaben gwamna da za a yi a jihar a ranar 10 ga Oktoba.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya yi wannan kiran a ranar Alhamis lokacin da ya yi wani zama a garin Akure da sarakunan da ke jihar kan batun zaben.

Yakubu ya ce an zo taron ne domin a nemi goyon bayan sarakunan don su ja hankalin talakawan su kan bukatar da ke akwai ta tabbatar da zaman lafiya da guje wa tashin hankali a dukkan tsawon lokacin da za a yi zaben da ma bayan zabe.
 
Ya ce: “A takaice, mu na neman tallafin ku ne ta hanyoyi uku. Na farko, ku ci gaba da kira ga jam’iyyun siyasa da ‘yan takara da magoya bayan su da su rungumi zaman lafiya, kamar yadda ku ka saba yi, a yankunan ku.

“Na biyu, ku yi kira ga al’ummar ku da su bi ka’idojin kare lafiyar su da ta jama’a daga kamuwa da cuta.

“Wannan zabe ne da za a yi shi a zamanin da ake fama da annobar cuta a duk duniya – wato annobar cutar korona. Ya na da muhimmanci ga masu zabe su kada kuri’ar su kuma su tafi gida ba tare da bata lokaci ba.

“Na uku, mu na neman addu’ar ku don a samu zaman lafiya a Jihar Ondo. Kuma mu na neman addu’ar ku ga INEC don zaben da za a yi a ranar Asabar ya kasance cikin lumana da adalci, kuma ba tare da nuna bambanci ba, sannan ingantacce.

“Zaben Edo ya yi kyau. Mun dukufa wajen ganin cewa na Ondo ma ya fi shi. Mun yi hakan a 2016. Wannan hukumar ta yi wancan zaben duk da fargabar da lullibe zukata kafin zaɓen.

“Ya na daga cikin zabubbuka mafi kyau da hukumar ta gudanar ta yadda ya kasance shi kadai ne zaɓen gwamna da aka yi a tarihin Jihar Ondo tun daga 1999 wanda ba a je kotu kan sakamakon sa ba.”

Farfesa Yakubu ya ce a yayin da ake gudanar da zaben a zamanin cutar COVID-19, INEC ta na ƙoƙarin ganin an yi shi lafiya lau, bisa shawarar Kwamitin Shugaban Kasa kan Cutar Korona da Cibiyar Yaƙi da Cututtuka ta Nijeriya.

Ya ce, “INEC za ta samar da takunkuman fuska, gilasan fuska, magungunan mantaleta da auduga saboda share injinan karanta katin zabe masu aiki da kwakwalwa a duk lokacin da aka tantance wani mai zabe, kuma za a samar da maganin fesawa a hannu.

“Kwamitin Shugaban Kasa kuma ya taimaka mana da na’urar auna ɗumin jiki da za a yi amfani da ita a kowace rumfar zabe.

“Duk da haka, a duk inda aka samu wani mai zabe ko ma’aikacin INEC ko jami’in tsaro ya nuna alamun kamuwa da cutar, to mun shirya da ‘yan Kwamitin Shugaban Ƙasa da ‘yan rundunar yaki da korona na Jihar Edo su yi saurin ɗauke wannan mutum zuwa cibiyoyin su inda su ke aje masu fama da cutar don a ba su magani.

“Daga darasin da na koya a Jihar Edo, na ga cewar mutane ba su kula sosai da bada tazarar da aka ce su rika ba junan su. 

“Mun yi amanna da cewa ku sarakuna masu martaba za ku iya taimaka mana wajen yin amfani da karfin muryar ku ku yi kira ga jama’a da su bi muhimman ka’idojin kiyaye lafiya.

“Hakan zai karfafa sakon da mu ka bayar cewa ba za a yarda wani mai zabe ya yi zabe ba har sai ya saka takunkumin fuska. Babu takunkumin fuska, babu yin zabe.”

Shugaban ya tabbatar wa da sarakunan cewa hukumar sa ta shirya sosai domin gudanar da zaben, ya na mai jaddada cewa INEC za ta kiyaye dokar ta ta ƙin nuna bambanci ga kowa a zaben kuma za ta yi aikin ta kamar yadda doka ta tanadar.

Ya ce, “Masu zabe a Jihar Ondo kadai ne za su yanke hukunci kan wanda zai zama gwamnan su na nan gaba a ranar Asabar, 10 ga Oktoba.”

Tun da farko a nasa jawabin a taron, Oba Frederick Akinruntan, wanda shi ne Olugbo na Ugbo kuma shugaban majalisar sarakunan gargajiya ta Jihar Ondo, ya yaba wa shugaban na INEC da ita hukumar kan aikin da su ka yi a zaben gwamnan Jihar Edo.

Daga nan Akinruntan ya yi kira ga hukumar da ta yi irin wannan aikin a Jihar Ondo wajen tabbatar da cewa an yi zaben cikin nuna rashin fifiko ko wariya, kuma cikin inganci.

Share.

game da Author