Jam’iyyar PDP da APC sun bude wutar yakin neman zaben gwamnan jihar Edo wurjanjan.
Yakin neman zabe ya yi zafin da har PDP ta yi amfani da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso wajen kamfen din kuri’un ‘yan Arewa mazauna Jihar Edo.
Ita kuma APC ta yi amfani da Gwamna Abdullahi Ganduje domin kokarin samun kuri’un ‘yan Arewa.
Yayin da Kwankwaso ya rika yawo kasuwanni da mazabun da ‘yan Arewa suka yi kaka-gida, ya kuma yi taro tare da shugabannin ‘yan Arewa mazauna Edo daga ko’ina ns lunguna da sakon Jihar.
Dukkan rangadin da ya rika yi, tare da Mataimakin Gwamna Shu’aibu ya rika yi.
Kwankwaso ya bayyana musu cewa ya je Edo ne domin ya ga ayyukan alherin da Gwamna Obaseki ya yi, kuma ya nemi ‘yan Arewa su sake zaben sa a karo na biyu.
“Na zo ne domin na taya dan’uwa na yakin neman zabe. Ina fatan za ku zabe shi domin ya kara rubanya ayyukan alherin da ya yi cikin shekaru hudu a wannan jihar.
“Jam’iyyar APC ba ta da wani karsashin da za ta yi yakin neman zabe da shi, sai bambancin addini da kabilanci kawai. Don haka kada ki bari ‘yan gayyar-Na’ayye su mulke ku.” Inji Kwankwaso.
Kwankwaso ya ce ya yi farin ciki da irin karbar da ‘yan Arewa mazauna Edo suka yi masa, kuma ya yi fatan PDP za su zaba.
Dama kuma a wani bidiyo da aka nuno Kwankwaso na jawabi a cincirindon jama’a da harshen Hausa a Benin, ya ce, kada su yarda a yi musu irin abin da aka yi wa Kano a zaben 2019.
Ya ce wadanda suka yi wa Kano rashin-mutunci suka murde zaben gwamna, su ne aka turo Edo, domin su maimaita abin da suka yi a Kano.
Don haka Kwankwaso ya ce, “A je a yi zabe, a saka, a kasa, a tsare. Kuma kada a bari a saci akwatin zabe.”
A bangaren Ganduje, wanda ya je wurin kamfen tare da dan takarar mataimakin gwamna, Gani Audu, ya yi kira da a zabi APC a zaben gwamnan jihar, domin a samu wanzuwar zaman lafiya a Jihar Edo baki daya.
Ya ce Ize-Iyamu mutum ne da tun tashin sa a Jihar ya yi karatu, kuma a ciki ya ke. Saboda haka kuma mutum ne mai kishi. Don haka a zabe shi.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda aka rika ragargazar Shugaba Muhammadu Buhari saboda ya bai wa Ganduje da rundunar sa jirgin shugaban kasa sun tafi Edo kamfen din APC da shi.
Discussion about this post