ZABEN EDO: Yadda masu zabe suka karairaya dokokin Korona a a rumfunan Zabe

0

Masu kada kuri’a a jihar Edo su karairaya dokokin Korona a runfunar zaben da ake gudanarwa a jihar ranar Asabar.

Hukumar zabe INEC ta yi bayanin cewa za ta samar da nauran gwada zafin jikin mutum domin a yi amfani da su a ofisoshin tattara sakamakon zabe dake kananan hukumomi da jiha.

Hukumar ta kuma ce za ta tilasta mutane saka takunkumin rufe fuska, bada tazaran mita biyu da amfani da man tsaftace hannu a lokacin da mutane za su zo kada kuri’un su a rumfunan zabe.

Sai dai wakilin PREMIUMTIMES ya rawaito cewa masu kada kuri’un dake kananan hukumomin Igueben, Esan, Ovia da Ikopba/Okha duk sun karya ka’idojin gujewa kamuwa da cutar korona da aka bada.

Masu kada kuri’u dake shiyar 06, rumfar zabe PU 08 dake makarantar firamaren ‘ Eguare’ Ebelle, Igueben sun kiyaye ka’idojin gujewa kamuwa da cutar.

Amma jami’an tilasta mutane su kiyaye sharaddun guje wa kamuwa da cutar dake rumfar zabe 08 Okpon, Shaya 02 dake karamar hukumar Ovia Kudu maso Yamma basu kiyaye ba. An ga dayawa suna gaggaisawa da hannu ba tare da sun iya yin komai ba.

Masu kada kuri’a dake rumfar zabe PU 8,9,10 dake karamar hukumar Kopba/Okha sun kiyaye sharuddan guje wa kamuwa a cutar.

Ma’aikatan hukumar INEC dake aiki a karamar hukumar Egor sun kiyaye sharaddun gujewa kamuwa da cutar.

Daga nan ma’aikatan hukumar dake aiki a shiyar 6, PU2, dake karamar hukumar Orhionmwon sun kiyaye sharaddun gujewa kamuwa da cutar.

Hukumar Zaɓe ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa ta kammala duk wani shiri da tsari da ake buƙata don tabbatar da an yi zaben gwamnan Jihar Edo cikin nasara a ranar Asabar din nan.

Share.

game da Author