ZABEN EDO: Sakamakon farko ya nuna APC ta shiga farauta da gurgun kare

0

Yayin da ‘yan takara tare da dimbin magoya bayan su ke zaman jiran sakamakon zabe, sakamakon da su ka fara fitowa daga rumfunan zabe daban-daban sun nuna PDP ta yi wa APC dukan rubdugun da in dai haka sakamakon zai rika fitowa, to APC ko gudu ba za ta iya yi ba, sai dai dingishi.

Sakamakon Mazabar Ohordua Primary School, W4, PU 008 da ke Esan ta Gabas, APC ta samu kuri’a 52, PDP 90.

Wani sakamako da ya fito daga Esan ta Yamma,, APC 24, PDP 97.

Daga Karamar Hukumar Esan ta Arewa maso Gabas, APC 51, PDP 125.

Rumfar zaben cikin Firamare ta Arue da ke Karamar Hukumar Esan ta Arewa maso Gabas, APC 8, PDP 350.

Wani sakamako daga rumfar zabe ta W9, Esan ta Yamma, APC 24, PDP 97.

Sakamakon farko-farko daga Karamar Hukumar Igueben ya nuna APC ta tabuka a Mazabar W 04, ta samu 117, PDP kuma 133.

A Mazabar W03 da ke Arue Primary School kuwa a Esan ta Arewa maso Gabas, PDP 250, APC 61.

Sakamakon farko daga Karamar Hukumar Owan ta Gabas, APC ta na da 123, PDP kuma 83.

A Mazabar Arue ta W 03, PDP 350, APC 8.

Sai daga Firamare ta Idunwele, Ewu 2, W 08, APC 88, PDP 178.

Share.

game da Author