Jam’iyyar APC ta sha kayi a kananan hukumomi 8 cikin 12 da aka bayyana zuwa yanzu.
Alkaluman zabe da aka bayyana zuwa yanzu sun nuna cewa baya ga nasarar da PDP ta yi a wadannan kananan hukumomi, ta ba APC rata mai yawan gaske da ya kusa zarce ƙuri’u 50,000.
A karamar hukumar Esan ta Kudu Maso Gabas, Obaseki na PDP ya samu ƙuri’u 10,565 shi kuma Ize-Iyamu ya samu ƙuri’u 9,237 votes.
A Esan ta Arewa Maso Gabas North-East, Gwamna Obaseki ya samu ƙuri’u 13,579, Ize-Iyamu na APC ya samu ƙuri’u 6,559 votes.
A Esan ta Tsakiya, Obaseki ua samu ƙuri’u 10,963, Ize-Iyamu ya samu 6,719. Karamar hukumar Igueben, Obaseki ya samu ƙuri’u 7,870, Ize-Iyamu ya samu ƙuri’u 5,199.
A Uhunmwode ta Kudu Maso Kudu, PDP ta samu ƙuri’u 10,022, APC ta samu ƙuri’u 5,972.
A Esan ta Yamma, Obaseki ya samu ƙuri’u 17,433, Ize-Iyamu ya samu 7,189.
A karamar hukumar Egor, gwamnan jihar Obaseki ya samu ƙuri’u 27,621, Ize-Iyamu na APC ya samu ƙuri’u 10,202.
Gwamna Obaseki ya samu ƙuri’u 41,030 a ƙaramar hukumar Ikpoba Okha, Ize-Iyamu ya samu ƙuri’u 18,218.
A Owan ta Gabas, APC 19,295, PDP 14,762. APC ta samu ƙuri’u 26,140 a karamar hukumar Etsako ta Yamma Obaseki kuma ƙuri’u 17,959.
A ƙaramar hukumar Akoko Edo, Obaseki ya samu ƙuri’u 20,101, Ize-Iyamu na APC ya samu ƙuri’u 22,963
A ƙaramar hukumar Etsako ta Gabas APC ta samu ƙuri’u 17,011, PDP ta samu ƙuri’u ta samu 10,668.
Gaba daya dai zuwa yanzu PDP ta samu ƙuri’u 202,574 a wadannan ƙananan hukumomi, APC ta samu ƙuri’u 154,704.
Discussion about this post