ZABEN EDO: Obasekin PDP ya ba Ize-Iyamun APC ratar kuri’u 86,000 bayan lissafa Kananan Hukumomi 16 a cikin 18

0

Yayin da aski ya kusa kawo gaban goshi, ɗan takarar jam’iyyar PDP, Gwamna Godwin Obaseki ya tsere wa na APC Ize-Iyamu da ƙuri’u sama da 86,000.

An bai wa APC wannan rata ce bayan an kidaya kuri’u na Kananan Hukumomi 16 a cikin Kananan Hukumomi 18 da ke jIhar.

Daga cikin Kananan Hukumomi biyu da ba a kai ga kidayawa ba, akwai Karamar Hukumar Orhionmwon, mahaifar dan takarar APC, Ize-Iyamu.

Obaseki ya tsere wa Ize-Iyamu fintinkau a zaben, wanda a yanzu sakamakon kananan hukumomi biyu kadai ake jira.

APC na da yawan kuri’u 202, 525. PDP kuwa 288, 572.

Idan ba a manta ba, a wannan Karamar Hukuma ce aka dankara wa jami’in INEC harbi da bindiga.

Share.

game da Author