Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yaba wa Hukumar Zaɓe ta Kasa (INEC) da hukumomin tsaro kan yadda aka gudanar da zaben gwamna na Jihar Edo a ranar Asabar cikin lumana.
Wike ya yi wannan yabon ne a lokacin da ya ke zantawa da ‘yan jarida a Gidan Gwamnati da ke Benin, babban birnin jihar.
Ya ce: “Yanzu ni dai ba ni da ikon bayyana sakamakon zaben, to amma daga rahotannin da mu ke samu zuwa yanzu daga wuraren da aka yi zaɓen, ina tsammanin dai mu na farin ciki.
“Ina so in yaba wa INEC zuwa yanzu saboda yadda su ka tabbatar da cewa jama’a sun kaɗa ƙuri’un su a rumfunan zae daban-daban.
“Ina kuma yaba wa hukumomin tsaro zuwa yanzu saboda yadda su ka tabbatar da cewa babu hatsaniya sosai, kuma idan aka ci gaba a haka ina tsammanin wani cigaba ne.
“Shi zabe, wani abu ne da ake yi mataki-mataki, ba a kai ga tattaro sakamakon ba tukuna; sai an tattaro sakamakon sannan za mu iya bada ra’ayin mu na ƙarshe.
“Zuwa yanzu dai, zan iya cewa sun yi daidai.
“Abin da mu ke cewa shi ne su tsaya tsayin daka kan abin da ya faru, kuma INEC ta tabbatar da cewa kada wani ya yi ƙoƙarin canza abin da mutane su ka zaɓa wa kan su; abin da mu ke cewa kenan. Idan jam’iyyar APC ce ta lashe zaɓen to a bar shi a haka. Idan kuma PDP ce ta lashe zaɓen, to shi ma a bar shi a haka.
“Ina dai jin mun ji dadin abin da ya wakana yanzu. Ina jin yanzu mu na da rumfunan zabe sama da guda 2, 000.
“Ina jin mu na farin ciki sosai kuma idan aka ci gaba a haka wannan zabe zai kasance ɗaya daga cikin mafi inganci da za a ce mun gani a Nijeriya.
“Ba wai kawai batun kaɗa ƙuri’a ba ne. Bayan kada ƙuri’a, ana ƙirga ƙuri’u, daga nan sai a tafi hada sakamako.
“Wannan shi ne mataki mai matukar muhimmanci, kuma lallai ne su tsare cibiyoyin su na tattaro sakamako daga matakin unguwa zuwa matakin daramar hukuma har zuwa matakin jiha saboda duk wanda ya yi zade zai ji daɗin cewa bukatar sa ta biya.”
A game da labarin da aka riƙa yadawa cewa sama da ‘yan sanda 300 sun kai masa farmaki a dakin sa na otal a garin Benin a ranar Juma’a, Gwamna Wike ya ce yanzu dai wannan lamari ya zama tarihi.
“Abin da ya faru jiya ya riga ya faru; yanzu kun gan ni, ban bar Edo ba,” inji shi.
Discussion about this post