Baya ga wakilai masu yawa da jaridar PREMIUM TIMES ta turo domin dauko labaran yadda ta kwaranye a zaben gwamnan jihar Edo, bangaren Cibiyar Zakulo Labaran Kwakwaf ta PREMIUM TIMES ya tura ‘yan-sa-ido har mutum 54.
An dora musu alhakin dauko rahotannin duk wani abin da aka aikata na ba daidai ba, kama daga bangaren jam’iyyun siyasa, jami’an tsaro, jami’an zabe da kuma jami’an gwamnatin jiha ko na tarayya, wadanda su ka yi duk wani kokarin kawo kafar-ungulu wsjen tabbatar da an gudanar da sahihin zabe.
An raba mutum uku a kowace Karamar Hukuma, daga cikin Kananan Hukumomi 18 na Jihar Edo.
Daraktan cibiyar ta PTCIJ, Tosin Alagbe ya roki al’ummar jihar Edo su yi zabe lami lafiya, su ba marada kunya, masu kallon cewa ba zabe za a yi a Edo ba, gangamin zubar da jini ne kawai za a yi.
Tuni dai aka fara jefa kuri’a a wasu mazabu da rumfunan zabe. Daidai lokacin da ake rubuta wannan labari, dan takarar APC, Ize-Iyamu ya jefa kuri’a.
Shi ma tsohon gwamnan jihar, kuma saukakken shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adam Oshiomhole an gan shi tsaye a kan layin jefa kuri’a.
An samu rahoton cewa a wasu kananan hukumomi masu jefa kuri’a da da jami’an zabe, ba su bi umarnin da Hukumar Dakile Cutar Korona (NCDC) ta bayar cewa jama’a su tsaya nesa da juna tazarar mita biyu tsskani ba.
Discussion about this post