ZABEN EDO: CDD da Yiaga Africa sun ce INEC ta gudanar da sahihin zabe

0

Kungiyoyin Sa-ido kan yadda aka gudanar da zaben gwamna a Jihar Edo na ci gaba da nuna amincewa da gamsuwar yadda zaben ya gudana a ranar Asabar.

Cibiyar Jaddada Sahihiyar Dimokradiyya (Center for Democracy Development, CDD), tare da Kungiyar Sa-ido Kan Zabubbuka da Dimokradiyya ta Afrika (Yiaga Africa), sun nuna gamsuwar su da yadda sakamakon zaben ya nuna.

Cikin wata sanarwar manema labarai da su ka fitar daban-daban, kungiyoyin biyu sun yarda cewa duk da dai akwai inda aka samu ‘yan kura-kurai da hatsaniya, zaben Edo ya nuna cewa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta kara inganta matakan gudanar da zabe sosai, fiye da wasu zabuka da aka gudanar a baya.

A zaben dai dan takatar jam’iyyar PDP, kuma Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki ne ya yi nasara da kuri’u 307, 955. Shi kuma dan takarar jam’iyyar APC, Pastor Ize-Iyamu, ya samu kuri’u 223, 619.

Yiaga ta jinjina wa INEC, sannan kuma ta nuna rashin jin dadin yadda a wasu wurare aka yi wa jami’an INEC din barazana a lokacin gudanar da zaben.

“Zaben Edo ya nuna an kara samun ci gaba sosai a bangaren INEC, idan aka kwatanta da zabukan jihohin Kwara da Bayelsa da aka gudanar cikin 2019.

“Mun san an samu ‘yan matsaloli nan da can, kamar lalacewar na’urar tantance masu rajistar zabe (card readers) da kuma rashin isar kayan aiki a wasu wurare da wuri.

“Amma wadannan kalubale ba za su hana a gamsu da sahihancin zaben ba.

“Yiaga na kira ga sauran ‘yan takara da su amshi kayen zabe, su gamsu cewa ba su yi nasara ba. Saboda sakamakon zaben ya nuna abin da al’ummar jihar su ka zaba ne aka bayyana.” Inji Yiaga.

Ita ma Kungiyar Sa-ido Kan Zabe ta CDD, cewa ta yi tabbas zaben sahihi ne, kuma karbabbe, kamar yadda Daraktar CDD Idayat Hassan ta bayyana, a cikin rahoton su bayan kammala zaben.

CDD ta ce duk da matsaloli kanana da hargitsi nan da can, zaben Edo ya zama sahihi, kuma ya fi inganci fiye da wasu zabuka na baya.

Kungiyar ta ce INEC ta yi rawar gani wajen jajircewar da jami’an ta su ka yi, a zaben wanda CDD ta ce ya tayar da jijiyoyi sosai a bangaren manyan jam’iyyu biyu, APC da PDP.

Har yau dai, CDD ta ce hatsaniyar da ta tashi a wasu wurare da jijiyoyin wuyan da aka rika tayarwa, ba abin mamaki ba ne, ganin cewa manyan ‘yan takarar biyu sauya jam’iyya su ka yi, inda wannan ya fice ya koma ta wancan.

A karshe Yiaga da CDD sun yi kira ga INEC ta gaggauta gyara matsalolin da ta fuskanta a lokacin zaben, musamman lalacewar ‘card readers’ da kuma rashin isar kayan zabe a wasu lunguna da wuri.

A wata sabuwa, Kungiyar Jam’iyyun Siyasa ‘Yan Hadin Kai, wato Coalition of United Political Parties (CUPP), ta yaba wa INEC kan rashin nuna bangIke game Ugochi Yerevan, ya fada cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja cewa matsayin hukumar wata alama ce da ke nuna dattaku a tsarin gudanar datsarina kasar nan.

Ugochinyere ya kuma yaba wa ma’aikatan INEC wadanda ya ce sun ki yarda da bukatar wasu ta a murde sakamakon zaben, ya ce hakan da su ka yi abin yabo ne.

Ya bayyana nasarar Obaseki da sunan nasarar da ikon jama’a ya nuna.

Ya ce: “Ba shakka wannan nasara ce da aka sha wuya kafin a same ta idan aka yi la’akari da tashin tashinar da aka shiga a fagen siyasar kasar nan kafin zaben.

“CUPP na kallon nasarar sake zaben Obaseki a karo na biyu a matsayin nasarar da jama’a su ka samu wajen zaben irin shugabannin da su ke so ba tare da wata tilastawa ba.”

Share.

game da Author