An yi wa ƴan jarida biyu duka, a rumfar zaɓen tsohon gwamnan Edo, Adams Oshiomhole, sabdoda sun dauki hoto lokacin da wani al’amari ke faruwa.
An doke su ne a rumfar zaɓe ta Mazaɓa ta 10, Uzairue ta Arewa maso Gabas) a rumfar zaɓe ta 1 da ke Karamar Hukumar Etsako ta Yamma.
Wakilin PREMIUM TIMES Samson Adenikan bai yi aune ba sai ji ya yi an falla masa mari, kuma ‘yan-sara-suka din su ka tsare shi na wani dan lokaci, saboda haushin ya dauki hotuna a lokacin da wani al’amari ke faruwa a rumfar zaben.
Wannan daukar hoto da wakilin mu ya yi ta harzuka ‘yan-sara-sukan da ke goyon bayan Oshiomhole.
Wakilin PREMIUM TIMES, Samson cewa ya yi ya ji saukar mari a fuskar sa, lokacin da ya ke kokarin daukar wani hoton inda ake sayen kuri’a da kudade.
Shi da wani dan jarida ne a ka yi wa dukan, awa daya bayan Oshiomhole ya jefa kuri’a ya bar wurin.
Kafin nan PREMIUM TIMES ta ruwaito yadda jam’iyyun APC da PDP su ka rika sayen kuri’u.
‘Yan sa-ido daga PREMIUM TIMES (PTCIJ) da ke wurin, sun ce yayin da ake sayen kuri’u lakadan ba ajalan ba, ejan din jam’iyya sun rika tirsasa dattawa zaben dan takarar su.
“Wasu gurza-gurzan karti ne su ka kewaye ni. Ban ankara ba sai kawai na ji an kifa min mari sau biyu. Har yanzu din nan jin fuska ta na ke ta yi nauyi. Su ka ce ba zan bar wurin ba sai na goge hotunan da na dauka.”
Ya ce sun ce masa idan bai goge hotunan ba, to sai dai a dauki gawar sa a wurin.
Ya ce ‘yan sandan da aka tura rumfar zaben su na tsaye Kamar gumaka su na kallon markabun da ake yi, amma ba wanda ya kai dauki.
Adenikan ya ce ‘yan APC ne su ka doke shi, domin sun rika yi masa burga cewa, “Kai ka san kuwa inda ka ke a nan? To mu nan ba sansanin PDP ba ne!”
Daya dan jaridar da aka lakada wa duka, ya na rahoto ne da gidan talbijin na GeeTV. Shi ma ya ci duka ne saboda taurin kai da ya nuna cewa babu wanda ya isa ya sa shi goge hotunan da ya dauka a wayar sa.
“Ya ci dukan tsiya, domin wani dan daba ma ya rafka masa kujera sau biyu a gadon bayan sa. Aka kwankwatse wayar sa, sannan aka kekketa masa rigar sa. Ya ji raunuka sosai.” Inji Samson.
An samu rahotannin tashe-tashen hankula da Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa, Farfesa Mahmood Yakubu ya ce za a dauki tsauraran matakin da ya dace kan sakamakon zaben da aka yi a wurin da aka yi hargitsi.