ZABEN EDO: Ɗan takaran gwamna na APC, Ize-Iyamu, ya ragargaza Obaseki na PDP a mazabar sa

0

Ɗan takaran gwamnan jihar Edo na jam’iyyar APC, Osagie Ize-Iyamu ya ragargaza abokin hamayyar sa na PDP, kuma gwamna mai ci a mazaɓarsa.

Da yake bayyana sakamakon zaben malamin zabe da ya kula da zaben wannan rumfa ta PU 26, Ward 5, Iguododo, dake karamar hukumar Orhionmwon ya ce APC ce ta yi nasara a wannan mazaba.

Kamar yadda sakamakon ya nuna, APC ta samu ƙuri’u 292, ita kuma PDP ta gwamna Osagie mutum 21 ne kacal suka zabe ta.

Ana nan dai ana ci gaba da bayyana sakamakon zabe a mazabun jihar zuwa yanzu.

Share.

game da Author