Babban sakataren ma’aikatan ilimi na jihar Anambra Nwabueze Nwankwo, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta bada umurnin a bude makarantun firamare da sakandare a jihar.
Nwankwo ya bayyana da haka a wani takarda da aka raba wa manema labarai ranar Juma’a garin Awka.
Gwamnati ta ce za a bude makarantun na tsawon wata daya domin dalibai su samu rubuta jarabawar su na zangon karshe na shekarar karatu na 2019/2020 daga ranar 14 ga Satumba zuwa 23 ga Oktoba.
Nwankwo ya ce iyaye za su samar da takunkumi fuska da man tsaftace hannu wa yaran su, sannan daliban dake makarantun kwana za su dawo makaranta a karshen mako kafin ranar da gwamnati ta bayyana.
Ya ce koyar da darussa da ake wa dalibai ta yanar gizo da gidajen talbijin za su ci gaba, dalibai kuma sai su zo su rubuta jarabawa.
Idan ba a manta ba, a farkon wannan mako ne gwamnatin jihar Kogi ta bayyana ranar 14 ga Satumba ranar da daliban jihar.
Kwamishinan ilimin jihar Wemi Jones ya sanar da haka a garin Lokoja yana mai cewa gwamnan jihar Yahaya Bello da kansa ya tsaida wananan ranar.
Jones ya ce gwamnati za ta canja tsarin darussan da ake koyar wa dalibai a makarantun jihar saboda canjin da aka samu.
Haka kuma suma jihohin, Oyo da Legas duk sun bayyana ranakun da za abude makarantu a jihohin.