ZAƁEN ONDO: Jami’an tsaro ɗauke da bindigogi za su tsare akwatinan zaɓe -INEC

0

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta bayyana cewa za ta yi amfani da jami’an tsaro 17,000 wajen gudanar da zaɓen gwamnan Jihar Ondo, wanda za a yi ranar 10 Ga Oktoba.

Sannan kuma hukumar ta ce za ta yi amfani da jami’an tsaro masu ɗauke da makamai su tsaitsaya kusa da rumfuna da akwatinan zaɓe, domin hana satar akwati da taka wa masu hargitsa zaɓe da gangan burki.

Kwamishinan Zaɓe Mai Lura da Yaɗa Labarai, Festus Okoye ne ya bayyana haka, a wurin taron yi wa ƴan jarida bitar makamar ɗaukar rahotannin al’amurran zaɓe.

An gudanar da taron bitar a Akure, babban birnin Jihar Ondo.

Okoye ya ce, “a baya ba a barin jami’an zabe su matsa kusa da akwatinan ko rumfar zaɓe dauke da makamai. Amma a yanzu mu na tattauna yiwuwar barin wasu riƙe da makamai su matsa kusa, domin hana sata ko fasa akwatin zaɓe.

“INEC ta damu matuƙa da yadda ake samun matsaloli na tsaro a lokacin zaɓe. Kuɗin inshorar rai bai kai darajar ran dan bautar ƙasa (NYSC) ba.” Inji Okoye.

Daga nan ya kara da cewa za a yi amfani da jami’an zabe 15,000, waɗanda suka hada da ‘yan NYSC da kuma daliban jami’a da na manyan kwalejojin gwamnatin tarayya.

“Sauran za su hada da rukunonin jami’an zaɓe daban-daban, wadanda su ma daga jami’o’i da manyan makarantu na Gwamnatin Tarayya za a dauko su.

Okoye ya ce INEC za ta tabbatar da an gudanar da sahihin zabe, kuma karɓaɓɓe. Don haka ne ma ya ce ba za a dauko jami’in tattara ƙuri’u ko da guda ɗaya daga cikin malaman manyan makarantun jihar Ondo ba.

Da ya koma batun zaɓen kuma, Okoye ya ce ba za a dage zaɓen saboda cutar korona ba, domin dokar Sashe na 80 cewa ta yi za a iya dage zaɓen gwamna idan ana yaki ne kawai.

Tuni dai idan ba a manta ba, INEC ta nuna cewa babu yadda za a yi ta ɗage zabubbukan jihohin Ondo da na Edo, domin yin hakan zai sa gwamnonin da ke kai su shige wa’adin ranakun da doka ta umarce su da su sauka daga mulki.

Share.

game da Author