Gwamna Godwin Obaseki na Jihar Edo kuma dan takatar zaben gwamna a karkashin jam’iyyar APC, shi da babban abokin gwabzawar sa na jam’iyyar APC Ize-Iyamu, sun bayyana dalilan da suka sa kowanen su ya sauya jam’iyya, a zaben wanda za a gudanar a ranar 19 Ga Satumba.
Shekaru hudu da suka gabata, Obaseki ne ya kayar da Ize-Iyamu a lokacin ya na APC, shi kuma Iyamu din ya na PDP.
Sai dai kuma a wannan zabe na 2020, yayin da Obaseki ya koma PDP aka ta shi takara a can, shi kuma Ize-Iyamu ys koma APC, kuma aka ba shi takara shi ma.
A wata muhawarar da Gidan Talbijin na Channels ya yi da su biyu din, kowanen su ya bayyana dalilin sauya shekar da ya yi.
“Na canja sheka daga APC zuwa PDP saboda an hana ni tsayawa takara a APC.
“Ai ina ganin duk duniya ta gani kuma ta san abin da ya faru da ni. Na je Ofishin Jam’iyya domin a tantance ni, amma aka ki. Ni kuma na koma PDP, kuma aka yi mini kyakkyawar karba.
“Ina jaddada matukar godiya ta ga jam’iyyar PDP, saboda karimcin da ta yi min, har ta ba ni takara.”
Haka Gwamna Obaseki ya bayyana, a lokacin da aka ce kowanen an ba shi minti daya tal ya fadi dalilin da ya sa ya canja jam’iyya.
Shi kuwa Ize-Iyamu, cewa ya yi da shi aka kafa jam’iyyar APC, amma ya fusata ya fice a 2014, saboda bai gamsu da yadda aka gudanar da zaben shugabannin jam’iyyar na jiha ba.
“Amma yanzu kuma na dawo. Ina godiya ga Ubangiji da ya ba ni ikon dawowa cikin APC. Dama ni dan gida ne, ba bako ba.”
Markabun gardandami sun tirnike a lokacin da ake yin fito-na-fito da sa-in-san kalamai a kan dalilin da ya sa su biyu din duk batun tsohon shugaban APC, Adams Oshiomhole ya dabaibaye su.
Obaseki ya ce, “Ni na fara hada gamayyar yadda aka tara wa Oshiomhole kudin kamfen, bayan ya sauka daga shugabancin Kungiyar Kwadago ta Kasa, ba shi da ko sisi, amma kuma ya tsaya takarar gwamna. Da ni mu ka taimaka masa ya zama gwamnan Edo.
“Na yi shekara takwas ina yi masa aiki ba tare da ana biya na ba. Lokacin da na zama Gwamna, sai ya nemi ya rika juya ni kamar yadda ake juya waina yadda ya ga dama. To daga nan ne sabani tsakanin mu ya shiga, har abin ya kai mu ga raba hanya gaba daya.” Inji Obaseki.
Sai dai kuma Ize-Iyamu ya karyata shi cewa bai bayar da gudummawar komai a kamfen din takarar gwamnan Oshiomhole ba, sai naira 100,000 kacal.
Discussion about this post