YUNWA: Akalla Yara sama da 150 za su yi fama da matsaloli na rashin lafiya a dalilin karancin maganin a Bauchi

0

Asibitin kula da yara kanana dake fama da yunwa na jihar Bauchi ta koka kan yadda karancin maganin warkar da yara dake fama da tsananin yunwa a jiki.

A dalilin haka yara 150 dake fama da matsalar yunwa za su fada cikin matsalar rashin lafiya.

Shugaban yi wa yara allurar rigakafi da kula da abincin da yara ke ci na asibitin Ado Manga ya ce asibitin ta raba lambobin wayan salula wa mutane domin su kira asibitin kafin su kawo yaran su asibitin.

“Mu yi haka ne saboda karancin maganin da asibitin ke fama da shi sannan da rage wa iyaye asarar Kudin mota da za su kashe zuwa asibitin sannan su zo kuma basu samu biyan bukata.

Manga ya ce asibitin ta wayar da kan mutane kan abinci irin na gargajiya wanda zai gina garkuwan jikin su.

Idan ba a manta ba a watan Janairu ne sakamakon binciken da KECCHD ta gudanar ya nuna cewa kashi 41.3 na yara kanana musamman ‘yan watanni shida zuwa shekara biyu a karamar hukumar Sumaila a jihar Kano na fama da yunwa.

Wani mamban kwamitin inganta kiwon lafiya na masarautar Kano (KECCHD), Dayyabu Muhammad ya bayyana haka.

Ya ce binciken ya nuna cewa kashi 48 bisa 100 na yara a jihar Kano na fama da matsanancin yunwa.

Muhammad ya fadi haka ne a taron da KECCHD da UNICEF suka shirya domin samar da mafita game da matsanancin yunwa da yara ke fama da shi a jihar.

Ya ce an shirya wannan taro ne domin wayar da kan sarakuna da uwaye kan irin rawar da za su iya takawa wajen ganin an kawar da yunwa a jikin yara.

Share.

game da Author