Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, Gambo Isa, ya bayyana wa manema labarai a Katsina cewa jam’ian ‘yan sanda sun cafke gogarman masu garkuwa da mutane a dajin Rugu dake Jihar Katsina.
Wannan hatsabibin dan ta’adda mai suna Abubakar Ibrahim, ya shahara wajen addabar mutanen yakin kananan hukumomin Batsari, Safana, Damnusa da Kurfi.
Gambo ya kara da cewa an ceto wasu mutum uku da ke tsare hannun masu garkuwa da mutane.
” Bayan Abubakar ya ja zugan wasu abokan aikata ta’addancin sa, zuwa wasu kauyukan Safana da kewaye, suka yi garkuwa da wasu mutane. Bayan haka dubun shi ya cika a wajen karbar kudin fansa na wani da suka yi garkuwa da.
Gambo ya kara da cewa zaratan jami’an tsaron SARS ne suka kama su.
Discussion about this post