YAJIN AIKI: Ƙungiyar Kwadago ta TUC ta haɗa karfi da NLC domin ƙara yawan masu zanga-zanga a ranar Litinin

0

Kungiyar Ma’aikata bangaren TUC, wato gamayyar ƙungiyoyi daban-daban, sun bayyana cewa za su shiga sahun uwar kungiya ta NLC ta Kasa domin fitowa kan titi a kasar nan a yi gagarimar zanga-zangar rashin amincewa da karin kudin man fetur da na wutar lantarki.

A makon jiya ne da TUC ta bada wa’adin mako daya ga Gwamnatin Tarayya, ko dai tw janye karin kudin fetur da na lantarki, ko kuma ma’aikatan kasar su fantsama yajin aiki.

Yayin da wa’adin ys kare a yau Laraba, TUC ta ce ta jingine fara yajin aiki a ranar 23 Ga Satumba.

Don haka ne ma ta ce za ta fito ta shiga sahun kungiyar NLC domin fitowa a yi gagarimar zanga-zanga a fadin kasar nan, a ranar Litinin, 28 Ga Satumba.

Shugaban Kungiyar Quadri Olaleye ne ya bayyana haka a taron da suka gudanar a Abuja, ranar Laraba, bayan cikar wa’adin barazanar da su ka yi wa Gwamnatin Tarayya.

Sakataren Kungiyar na Kasa, Muda Lawal-Ozigi, ya yi kira ga manyan kasashen duniya irin su Amurka, Birtaniya, Jamus su hana manyan ‘yan siyasar Najeriya da su ka sace kudin kasar nan shiga kasashen su.

“Ba za mu taba yarda da karin kudin fetur da na wutar lantarki ba.

“Nan APC ta rika yawo cikin 2014 da 2015 lokacin zabe ta na yi wa jama’a alkawarin za ta gyara matatun mai. Ashe abin duk yaudara ce kawai.”

Ya kuma koka a kan yadda har yau akwai jihohi 8 a kasar nan da su ka kasa biyan mafi kankantar albashi na naira 30,000.00.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda Kungiyar Kwadago ta NLC ta buga tambarin yin gagarimar zanga-zangar kin yarda da karin kudin wuta da na fetur.

Kungiyar Kwadago ta Kasa, NLC ta bayyana cewa dukkan ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kan su day sauran jama’a, kowa ya fito zanga-zanga a ranar Litinin 28 Ga Satumba, har sai Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta janye nunkin kudin wutar lantarki da ta yi, kuma ta janye karin kudin man ferur tukunna.

Majalisar Gudanarwar Kungiyar Kwadago ce ta amince da yin gangamin fara zanga-zangar, bayan da Babban Kwamitin Zartaswar kungiya ya rattaba hannun cewa kawai a fita a fara zanga-zanga, har sai gwamnati ta janye karin na kudin fatur da na wutar lantarki.

Sai dai kuma ba a sani ba ko daga zanga-zangar za a zarce yajin aiki ne tukunna. Amma dai Kungiyar Kwadago din ta bayyana wa manema labarai cewa su jira za a fitar da takardar bayan taron gaggawa tukunna.

PREMIUM TIMES ta buga labari a makon da ya gabata, wanda ta ruwaito NLC sun bai wa Gwamnatin Tarayya gargadin wa’adin makonni biyu ta janye karin kudin wutar lantarki da na fetur.

Fetur dai a yanzu ya koma naira 161, alhali Buhari tun farko kafin ya hau mulki, alkawari ya yi cewa zai rage kudin sa na lokacin daga naira 87 kowace lita, zuwa naira 40.

A halin yanzu kuma kudin wutar lantarki ya nunka, har da unguwannin da Hukumar Raba Wutar Lantarki ta Kasa ta ce su karin bai shafe su ba.

Kafin a yi kari, unguwannin talakawa ana sayen ‘unit’ 32 a naira 1,000. Yanzu kuwa guda 16 ne a naira 1,000.

Da ya ke wa manema labari jawabi a Abuja a ranar Talaba, Shugaban Kungiyar Kwadago ta Kasa ya yi tir da karin kudin wuta da na fetur. Sannan kuma ya yi kira ga gwamnati ta gaggauta janye karin.

Ya kuma yi kira da a gaggauta gyara matatun mai na kasar nan.

A yanzu dai ana kan gyaran su, amma ba su iya tace danyen mai. Ko an gyara din ma ba za su iya tace adadin wanda Najeriya ke bukata a kullum ba.

Gwamnatin Buhari dai ta ce ta daina bayar da tallafin kudin fetur ne ga dillalan mai, shi ya sa ta yi karin, domin cike gibin da take biya don talaka ya samu sauki.

Share.

game da Author