Tsohon Kakakin Yada Labarai na tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan, wato Reuben Abati, ya cire mayafin kunya, inda ya rika gantsara batsa a Gidan Talbijin na ARISE TV, ya na bayyana muhimmancin Azzakarin namiji.
Abati, wanda ya yi kasassabar a lokacin da su ke gabatar da wani shiri a gidan talbijin din, ya na magana ne a kan rahoton cewa Kwamandan ‘Yan Sandan Ghana ya gargadi ‘yan sandan kasar su rage jima’i domin su samu kuzarin yin aiki tukuru a looacin zabe mai zuwa nan da wata biyu a kasar.
Kwamandan Shiyyar ‘Yan Sandan Accra, Afful Boakye-Yiadom ne a ranar Litinin ya shawarci ‘yan sandan shiyyar cewa su daina jima’i domin samun kuzarin da za su yi aikin sa-ido a lokacin zaben da za a gudanar cikin watan Disamba.
“Duk wanda haka kawai zai hana zakarin namiji yin aikin sa, ai kamar ya kassara jima’i ne baki daya.
“Kai shi fa zakari ba abin wasa ba ne. Domin su Girkawa da Romawa sun dauke shi da darajar da har ma bauta masa su ke yi.” Inji Abati.
Daga nan Abati ya riika zayyana sunayen wasu mashahuran marubutan da su ka rubuta litattafai a kan darajar azzakari, kuma abin mamaki duk da ka ya rika furtawa, ba karantowa ya rika yi ba.
“Akwai wani littafi mai suna Tarihin Azzakari, kuma akwai wani littafin da Tom Hickman ya rubuta mai suna ‘Ajiyar Ubangiji: Rayuwa da Tasirin Azzakari”.
“Amma idan abin da aka fi karkata a kai, shi ne matsayar da David Friedman ya dauka a kan Azzakari, a cikin littafin sa mai suna, “Zandareriyar Sanda Mai Tunani Da Kanta”.
Haka Abati ya bayyana aka nuno shi kai-tsaye kowa na kallo ya na barka batsa a talbijin.
Ya karkare da wani littafi mai suna, “Tarihin Azzakari A Al’adance”, inda ya nuna cewa azzakari ya na tunanin kan sa da kan sa.
“Saboda haka ban san dalilin da zai sa wani wannan kwamandan ‘yan sanda ya nemi yin shisshigin shiga sha’anin zakari ba, har ya hana shi aikin da. Wannan ai karambani da shisshigi ne, kuma da shiga gonar da ba ta sa ba.” Inji Abati.
Discussion about this post