Tsohon mai tsaron gida na Ƙungiyar Super Eagles, Ike Shorunmu, ya bayyana takaicin yadda likitoci suka yi watsi da bukatar gaggawa, har suka bar tsohon ɗan wasan Super Eagles, Ajibade Babalade ya mutu a kofar shiga asibiti.
Shorunmu, ya shaida wa manema labarai a Ibadan cewa, ciwon bugun zuciya ya kama Babalade farat-daya. An garzaya da shi wani asibitin kudi, Amma a karshe suka ki karbar sa.
Ya ce haka tilas ga Babalade a cikin halin tagayyara, amma aka sake kinkimar shi zuwa Asibitin Jami’ar Ibadan.
“An fara kai shi wani asibitin kudi ne, amma sai likitoci suka ki duba shi, duk kuwa da halin da ya ke a ciki.
“Sun ce a kai shi Univery College Hospital’. Amma kafin a shiga harabar asibitin sai ya rasu.” Inji Shorunmu.
Bai dai bayyana sunan asibitin da jam’an asibitin suka ki karbar Babalade din ba
Babalade ya mutu ya na da shekaru 48 a duniya. Shi ne mai tsaron bayan Najeriya na wani lokaci.
Ike Shorunmu ya ce a ranar Juma’a aka sanar da shi rasuwar Babalade.
“Da na shiga Sallar Juma’a sai na kashe waya ta. Amma ina budewa bayan gama Sallah, sai aka kira waya ta, aka fada min. Ina yi masa addu’a Allah ya gafarta masa.
Sau da yawa a Najeriya ana korafi da yadda jami’in kula da lafiya da likitoci kan ki duba marar lafiya, har ya kai ga mutuwa.
An fi samun irin haka a lokacin da aka kai wadanda su ka yi hadari. Likitoci kan ki duba su, a ce sai an hada da ‘yan sanda.