Yadda Sojan Najeriya ya bindige kan sa bayan an ladabtar da shi bisa zargin satar da ya ce bai aikata ba

0

Wani Sojan Najeriya mai muƙamin ‘Lance Corporal ya kashe kan sa bayan na gaba da shi sun ladabtar da shi, bisa zargin ya saci wayar hannu, wadda ya yi ikirarin ba satar ta ya yi ba.

Lamarin ya faru tun a ranar Alhamis, inda sojan mai suna Lance Corporal Victor Ojeamiran, wanda ke yakin Boko Haram a Birgade ta Army Task Force Brigade 27 da ke Buni Gari, a Karamar Hukumar Gujba, Jihar Yobe.

Ganau ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa Ojeamiran ya dankara wa kwakwalwar sa harsashi, bayan ya tura wani Sajen da wasika ya kai wa ogan su a Task Force din.

Sai dai majiyar ta nemi PREMIUM TIMES ta sakaya sunan sa, domin kada manyan sa su yi masa bi-ta-da-kulli.

Wasikar dai kamar yadda PREMIUM TIMES ta gano, ya rubuta ta ne a matsayin nuna wa iyalin sa da duniya cewa shi ba barawon wayar GSM ba ne, kamar yadda aka zarge shi, kuma aka hana shi kare kan sa.

Buni Gari ya na da tazarar kilomita 7 daga hedikwatar Task Force ta 27 da ke Buni Yadi, garin da aka gina ‘Army Special Forces School, cikin Karamar Hukumar Gujba.

Yadda Aka Tozarta Sojan A Bainar Jama’a Bisa ‘Kazafi’:

Shi dai sojan ya je Damaturu ya sayo wayar GSM, wadda aka rigaya aka fara amfani da ita, wato ‘second hand’.

Majaya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa ashe wayar ta wani babban Jami’in soja ce aka sata a Damaturu.

Sojan ya yi amfani da na’urar zamani ya bi sawun wanda ya sayi waya, wato soja Victor, bayan ya koma bariki da waya.

An ce wannan babban soja ya rika ladabtar da Victor a gaban jama’a, har ta kai farar hula su na daukar bidiyon da wayoyi, su ka rika turawa a soshiyal midiya.

Victor Ojeamiran ya kasa daure tozartawar da aka yi masa, musamman yadda aka rika watsa bidiyon.

Hakan ya sa shi tunanin cewa ba zai iya fuskantar iyalin sa ba, bayan an bata masa suna, ana yi masa kallon barawo.

Yayin da Kakakin Sojojin Najeriya, Sagir Musa ya ce labarin bai isa gare shi ba tukunna, kakakin 27 Task Force, Chinonso Oteh wani Laftanar, ya yi alkawarin zai tuntubi wakilin mu da bayanin lamarin daga Hukumar Sojoji. Daga nan ko wakilin mu ya kira wayar ba ya dauka.

Amma wannan jarida ta tabbatar da cewa jami’an soja sun shigar da bayani cewa ya kashe kan sa ne ranar Lahadi, 20 Ga Satumba.

Sannan sun fitar da sanarwa cewa ana binciken musabbabin yadda abin har ya kai shi ga kashe kan sa.

Share.

game da Author