Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana abubuwan da suka faru har ya yi asarar kujerar sa a lokacin zaben 2019.
Saraki ya dade ana damawa da shi a siyasar Jihar Kwara, inda ya zama gagarabadau, shekaru bayan ya yi gwamani jihar tsawon shekaru takwas.
Sai dai kuma a zaben 2019 an yi masa taron-dangin da ya yi sanadiyyar rasa kujerar sa ta Sanata da kuma kwace masa ragamar siyasa a jihar baki daya, akalla na tsawon shekaru hudu da ake ciki.
A cikin jawabin da ya gabatar yayin da kungiyoyin kare dimokradiyya su ka gaggace shi taron Ranar Tunawa da Dimokradiyya ta duniya, a ranar Talata, ya yi jawabin yadda ya karbi kaddarar faduwa zabe, duk kuwa gurguzun fashin kuri’u da ya ce an yi masa.
“Na shiga zaben 2019 amma ni da jam’iyya ta PDP, duk aka kayar da mu. Na ce mu hakura duk da mu na da hujjojin yadda Gwamnatin Tarayya ta shiga da karfin ta, ta yi kane-kane. Kuma mu na da sauran hujjojin yadda aka yi amfani da wasu hanyoyin da ba su dace ba, wadanda doka ta haramta, aka murkushe zabe na.”
Ya ce kowa ya ga irin yadda APC ta nuna maitar ta a fili, wajen ganin sai ta kwace kujera ta da ta gwamnan Kwara, ko da tsiya ko da tsinin tsiya”.
“Mugayen bakaken kalaman da Shugaban APC na lokacin, Adams Oshiomhole ya rika yi cewa duk ma hanyar da za su bi don su kwace gwamnatin Kwara, sai sun bi domin kawai su karya-lagon siyasa ta. Duk mun yi rikodin, mun ajiye a matsayin hujja.
“Amma duk da haka na daure, na danne zuciya ta, na ce wa magoya baya na banda rigima, mu karbi kaddara.
“Ban je kotu ba. Maimakon haka, sai na taya wanda ya yi nasara murna. Don dai dimokradiyya ta dore a tafi ba tare da tazgaro ba.”
Da ya koma kan zaben Gwamnonin Edo da Ondo da za a yi kwanan nan kuma, Saraki ya yi kira ga Buhari ya tabbatar an yi adalci, domin wadannan zabukan su ne zakaran-gwajin-dafin mutunci idan ya sauka daga mulki nan da shekaru biyu masu zuwa.
Discussion about this post