Bayan nasarar da ya samu wajen shirya zaben gwamnan Jihar Edo a ranar Asabar da ta gabata, Shugaban Hukumar Zabe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bada tabbacin cewa sun shirya tsaf domin gudanar da zaben gwamna da za a yi a ranar 10 ga Oktoba a Jihar Ondo.
Yakubu ya fai haka ne a Akure, babban birnin Jihar Ondon, a ranar Laraba, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewar shugaban ya je Akure ne don ziyarar kwana uku saboda duba shirye-shiryen da ofishin hukumar ke yi don gudanar da zaben, ya kuma gana da masu ruwa da tsaki a zaben.
Farfesa Yakubu, wanda ya ce ya je jihar ne domin ya sadu da ma’aikatan hukumar da ke jihar, ya kara da cewa duk da matsalar gobara da aka samu a ofishin INEC na jihar, hukumar ta gama duk wani shiri saboda zaben.
Ya ce: “Mun riga mun murmure. Sai dai abin bakin ciki shi ne mun yi asarar injinan karanta katin zabe masu aiki da ƙwaƙwalwa har guda 5,000 amma mun murmure ta hanyar sake samo injinan da ake bukata daga Jihar Oyo da ke makwabtaka da nan, kuma an kawo su nan.
“Sun iso, an yi cajin su kuma an yi masu saiti, an shirya su domin zaben da za a yi a ranar 10 ga Oktoba a Jihar Ondo.
“Abu muhimmi shi ne za mu yi amfani da komfutocin ‘Z-pads’ wajen tura sakamakon zaben kai-tsaye a ranar zaben, kuma mun dauko wadannan ‘Z-pads’ ɗin daga Edo zuwa Jihar Ondo saboda zaben.
“Saboda haka, irin shirye-shiryen da mu ka yi a Edo, su ne kuma mu ka yi a Ondo, saboda haka mun shirya wa zaɓen.”
Yakubu ya ce zai hadu da majalisar sarakunan gargajiya da hukumomin tsaro da jami’an hukumar a Yankunan Kananan Hukumomi 18 da ke jihar musamman saboda zaɓen.
Ya ce, “ Wannan ita ce ziyarar farko da na kawo. Za mu sake dawowa bayan mako daya don babban taro da za mu yi da masu ruwa da tsaki da kuma rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.”
INEC dai ta yi asarar komfutocin karanta katin zabe guda 5,141 da za a yi amfani da su a zaben na ranar 10 ga Oktoba a Jihar Ondo lokacin da wuta ta tashi da dare a ofishin hukumar a Akure.