Yadda kayan abinci su ka kara tsada da kashi 16% cikin watan Agusta

0

Kayan abinci sun kara tsada zuwa kashi 16% a cikin watan Agusta, idan aka kwatanta da tsadar su zuwa kashi 15% a cikin watan Yuli. Hukumar Kididdigar Alkaluman Bayanai ta Kasa (NBS) ce ta bayyana wannan rahoto, a ranar Talata.

Rahoton ya ce karin farashin kayan abincin da aka samu a cikin tsakiyar watan daga kashi 12.82 zuwa 13.22 shi ne mafi tsanani cikin shekaru biyu.

Karin tsadar kayan abinci ita ce musabbabin tsada da kuncin rayuwar da aka fuskanta a fadin kasar nan.

Sama da shekara uku kenan farashin kayan abinci ke kara tashi, yayin da ya ke ci gaba da kara tsadar rayuwa a kasar nan.

Karin farashin abinci a cikin watannin nan dai na ci gaba da faruwa ne, tun bayan barkewar annobar Korona, wadda ta hana gudanar da harkoki, komai ya yi tsaye cak.

Amma gwamnatin tarayya ta ce ta na tattalin arzikin zai dan mirmire da kashi 8 9 a wannan shekara.

A watannin Afrilu da Mayu da Yuni dai an yi kintacen tattalin arziki ya cakire da kashi 6.1. Kamar yadda NBS ta bayyana.

Haka Babban Bankin Najeriya, CBN ya ce tattalin arzikî kasa zai iya karuwa da kashi 14.15 nan da zuwa karshen Disamba.

“Wannan tsada ta kara tsawwala musamman a bangaren kayan masarufi irin su biredi, sarelak, dankali, daya, rogo da sauran abinci irin su nama, kifi, kayan marmari, man girki da su kayan miya.

Haka bayanin kididdigar farashin kayan abinci da NBS ta yi ya bayyana a ranar Talata.

Daidai lokacin da ake fama da kuncin rayuwa, tsadar kayan abinci da karin farashin fetur da wutar lantarki, ‘yan Najeriya na fama da bala’in ambaliyar ruwa wanda har yanzu ya ke ta barna a gonaki, gidaje, garuruwa da birane.

Farkon watan Satumba PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin da Shugaba Muhammdu Buhari ya nuna tsananin damuwa da takaici ganin yadda farashin kayan abinci ke ci gaba da yin tashin-gwauron-zabo a kasar nan.

Buhari ya ce inda ma abin ya fi kara damun sa, shi ne yadda farashin ke ci gaba da tashi a daidai lokacin da tattalin arzikin Najeriya ke tafiyar hawainiya, sakamakon tarnakin da cutar Coronavirus ta yi wa tattalin arzikin Najeriya.

Wannan damuwa ta Shugaba Buhari, ta na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na Fadar Shugaban Kasa, Garba Shehu ya fitar a ranar Laraba.

Sanarwar ta fito ne a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke zaman makokin karin kudin wutar lantarki, sannan kuma a ranar da aka bada sanarwar karin kudin fetur.

Tuni dai har masu gidajen mai a garuruwa har da Abuja sun fara sayar da lita daya a kan naira 161.

Tun a rranar Laraba bayan NNPC ta yi sanarwar kara wa fetur kudi zuwa 151 farashin sari, sai IPMAN, wato Kungiyar Dillalan Fetur Masu Zaman Kan Su, suka fitar da sanarwar cewa sun yanke shawara za su sayar da lita daya a kan N161.

IPMAN ta ce a haka ne kadai za su iya cin riba idan suka sayi lita 1 kan Naira 151 daga gwamnati.

Sanarwar ta ce “Shugaba Muhammadu Buhari, ya nuna damuwar gwamnatin sa game da hauhawar farashin kayan abinci a fadin kasar nan a daidai lokacin da tattalin arzikin kasar ya ke cikin halin kunci sakamakon matsalolin da annobar korona ta jawo a fadin duniya.

Buhari ya bai wa ‘yan Najeriya tabbacin cewa wannan halin kunci na tsadar kayan abinci abu ne na dan lokaci, ba mai dorewa ba, inda ya kara da cewa gwamnatin sa ta fara nema tare da kafa matakai na saukaka lamarin.

Tsadar Abinci: Laifin ‘Yan Kasuwa Ne -Buhari

Shugaba Buhari ya waiwaya kan ‘yan kasuwa, ya zarge da cewa su ne ummul-haha’isin jawo karanci da tashin farashin kayan abinci a kasuwanni.

“Duk da ya ke Allah ya taimake mu an sami isasshen ruwan sama wanda tsammanin samun kyakkyawar damina kan kai ga faduwar farashin kayan abinci tare da sauaka wa al’umma, damuwar gwamnati a nan ita ce dabi’ar cutarwa a zukatan wasu ‘yan kasuwa ta yi matukar karuwa a tsakanin ‘yan kasuwa a cikin ‘yan shekarun da suka gabata. Hakan ke sa a ga saukin da za a samu ya zama na dan kankanen lokaci.”

Shugaba Buhari ya ce daga cikin matsalolin da aka samu a kakar bana, wadanda suka faru sakamakon bullar annobar cutar Korona da ta shafi duniya baki daya, har da jinkirin da aka samu wajen sayo kayayyakin hadi na samar da takin zamani a gida da kuma mugun halin wasu kamfanonin sarrafa shinkafa, wadanda kan biya kowane nau’in farashi don ganin cewa shinkafar ba ta yanke a kamfanonin su ba.

Buhari ya ce an gano cewa mafi yawan lalatattun dillalan da ke haddasa karancin kayan abinci ta hanyar saye daga hannun manoma sannan su sayar ga jama’a a kan matsanancin farashi, ba ‘yan Najeriya ba ne, ‘yan kasashen waje ne.

“Yanzu haka Shugaban Kasa ya bayar da izinin fitar da kayan abinci daga rumbunan ajiyar kayan abinci na gwamnati, da suka hada da tan 30,000 na masara ga kamfanonin da ke yin abincin dabbobi don saukaka tsadar kiwon kaji.

“Shugaba Buhari ya tattauna wasu daga cikin wadannan al’amurra tare da ƙungiyoyin masu samar da abinci da abin ya shafa, musamman manoman shinkafa da sauran nau’ukan abinci na tsaba.

“Da haɗin kan su, ba da dadewa ba hauhawar farashin kayan abinci zai zama tarihi.”

Share.

game da Author