WUTA SALLAU’: Ƙungiyar Kwadago ta yi fatali da karin kuɗin wutar lantarki

0

Ƙungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), ta yi kira ga Hukumar Ƙayyade Makamashin Lantarki ta Ƙasa (NERC) cewa ta ɗauki tsatstsauran mataki a kan kamfanonin saida wutar lantarki (Discos), saboda karin kuɗin lantarki.

Shugaban NLC na ƙasa, Ayuba Wabba ne ya yi wannan kira a Abuja cikin wata sanarwar da ƙungiyar ta raba wa manema labarai.

Wabba, a cikin sanarwar ya bayyana cewa karin kudin wutar lantarki “raina wa ‘yan Najeriya hankali ne, kuma ana kokarin tura su a kai su bango.”

Ya ce kungiyoyin kwadago daban-daban za su ja zugar ma’aikatan Najeriya domin fitowa zanga-zangar rashin amincewa da karin kudin hasken lantarki da kamfanin saida wuta na Abuja (AEDC) ya yi, tun daga ranar 1 Ga Satumba.

“NLC ta yi tofin Allah wadai dangane da yadda Hukumar Kula da Makamashin Lantarki (NERC) ta nuna ba ta damu da duk halin kara wa jama’a kudin wuta da ake ciki.

“Sabon karin kudin wuta shirme ne da rashin tausayi. Saboda haka ba za a yarda da shi ba.

“Ya kamata Hukumar NERC ta sani cewa matsawar ta yi galala ta bar wani kokirzo ko wasu ‘yan kadubar zuba jari su rika suka rika shan jinin Najeriya, to sunan NERC zai baci gaba daya.

“Yan Najeriya na da hakkin bukatar NERC ta tsaya ta kare musu hakkin su wajen batun lantarki a kasar nan.”

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin cewa daga yanzu bankuna za su rika karbar kudin wuta, ba kamfanonin bada hasken lantarki ba.

Babban Bankin Najeriya (CBN), ya hana kamfanonin saida wutar lantarki (Discos) karbar kudaden wuta ya maida aikin karbar kudaden a hannun bankuna.

Daraktan Kula da Bankuna, Hassan Bello ne ya bayyana haka, tare da cewa kwamitin lura da harkokin lantarki na kasa ne ya cimma wannan matsaya, domin a kauce dimbin matsalolin da aka rika fuskanta wajen tara kudaden.

Sanarwar ta ce daga yanzu za a rika biyan kudin wuta ne kai-tsaye a bankuna, daga nan sai banki ya biya kamfanonin saida wa jama’a wutar lantarki. Kuma banki zai biya Hukumar Raba Wutar Lantarki na ta kudin kai-tsaye.

Sanarwar ta hana kamfanonin saida wuta Discos karbar kudaden wuta ko wasu kudaden harkokin lantarki na Discos din.

CBN ya jaddada cewa asusu ne za a bude mallakin Hukumar Kula Da Hasken Lantarki ta Kasa, Hukumar Rarraba Hasken Lantarki ta Kasa da kuma Kamfanonin Saida Wutar Lantarki (Discos) su 11 da ake da su a kasar nan.

CBN ya ce ana kwana ana tashi kullum Discos na fuskatar matsalar karbar kudaden wuta. Shi ya da bashin da Discos din ke karba ya yi yawa matuka.

Takardun bayanai sun tabbatar ana bin kamfanonin saida wuta (Discos) su 11 bashin naira bilyan 622. Sai kuma kudin ruwan da suka rika taruwa, har a yanzu suka kai naira bilyan 308.

Sabon Tsarin Wutar Lantarki:

Gidan Radiyon BBC ya yi hira da jami’in yada labarai na KEDCO, mai kula da Kano da Jigawa, inda ya ce: “Sabon tsarin ya karkasa masu amfani da wutar zuwa gida biyar inda karfin aljihun kowa ne ma’aunin wutar da za a ba shi.”

Mai magana da yawun kamfanin raba wutar lantarki da ke kula da jihohin Kano da Katsina da kuma Jigawa, Ibrahim Sani Shawai, ya shaida wa BBC, cewa an karkasa tsarin ga bangarori daban-daban ciki har da masana’antu da kamfanoni da ma’aikatun gwamnati da kuma unguwannin masu hannu da shuni.

Sai dai ya ce mutane na da damar komawa matakin koli na samun wutar lantarki idan suka ga suna da karfin biyan abin da ake caza.

Ga yadda matakan suke:

“Mataki na A: Wadanda ke wannan mataki za su samu wutar lantarki ta tsawon awanni 20 zuwa sama.

Mataki na B: Na bada damar samun wutar lantarki ta tsawon awanni 16 zuwa 20.

Mataki na C: A wannan mataki za a samu wutar lantarki ta tsawon awanni 8 zuwa 12.

Mataki na D: Awa 4 zuwa awa 8

Share.

game da Author