A daidai kungiyar kwadago ta Kasa da sauran kungiyoyin dake tare da ita na shirin fitowa ranar Litini mai zuwa domin yin zanga-zangar nuna fushin su ga karin kudin man fetur da gwamnatin Najeriya tayi da na wutan lantarki, kotu ta dakatar da wannan zanga-zanga.
Alkalin Kotun Ibrahim Galadima ya gargadi kungiyar da makarrabanta kada su kuskura su hana mutane zuwa aiki ko kuma garkame wuararen aiki a kasar nan kamar yadda suka shirya yi ranar Litini 28 ga Satumba har sai kotu ta gama sauraren karan ranar tsaida wannan shari’a.
Haka kuma kotun gargadi sauran kungiyoyin kare hakkin ma’aikata dake aiki tare da kungiyar kwadago ta Kasa, cewa kada su kuskura su hana ma’aikata shiga wuraren aikin su ranar 28 ga wata, har sai an warware sannan an samu matsaya ga shari’ar dake gaban kotu.
Wata kungiyar samar da zaman lafiya ne shigar da kara kotu tana neman a dakatar da wannan shiri na yin gangamin zanga-zanga domin tilastawa gwamnati ta janye karin kudin mai da na wutan lantarki da ta yi a kasar.
Lauyan kungiyar Sanusi Musa ya shigar da karar.
Bayan haka kotu ta umarci Sufeto Janar din ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro, su samar wa Najeriya tsaro a wannan rana, kada wani ya hana su shiga wuraren aikin su.
Kungiyar Kwadago bata ce komai ba tukunna, ko tana nan akan bakanta na yin zanga-zangar kamar yadda ta shirya a mako mai zuwa ko kuma akwai wani abin da take shirya wa daban.