TSANANIN KISHI: Yadda Jamila ta kashe Ɗan kishiyarta a Kano – NAPTIP

0

Hukumar Yaki da Safarar Mutane ta Kasa (NAPTIP) reshen jihar Kano ta bayyana yadda ta damke wata matar aure Jamila Abubakar mai Shekarau 29 da ake zargi da laifin kashe dan kishiyarta da tsananin duka.

Shugaban hukumar Shehu Umar ya Sanar da haka wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a makon jiya a garin Kano.

Umar ya ce hukumar na zargin Jamila da kashe dan kishiyarta Muhammad Bashir mai shekaru 7 da dukan tsiya a gidan su dake Tarauni Kasuwa.

Ya ce kafin haka ya faru hukumar ta gargadi Jamila da mijinta kan yadda suke azabtarwa da cin zarafin wannan yaro.

“A kwanakin baya hukumar NAPTIP ta samu labarin yadda Jamila ke cin zarafin wannan yaro ta hanyar rashin bashi abinci da kula da shi.

“Saboda ɗiban albarka irin na Jamila idan za ta fita gida sai ta daure Bashir a wani turke da ta yi masa kamar dabba.

“Jamila da mijinta sun yi alkawarin kula da yaron bayan wannan gargadi da hukumar ta yi musu. Da yake ba da gaske ta ke yi ba sai gashi wata rana ta na cikin muzguna masa sannan ta dukar Bashir sai rai yayi halin sa, Bashir ya ce ga duniyar ku nan.

Umar ya ce NAPTIP ta mika wa rundunar ƴan sanda wannan magana domin ci gaba da bincike akai.

Share.

game da Author