TSADAR RAYUWA: Motar Buhari Ko ‘Motar Alpha’?

0

Ko lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya ki maida hankali ga lamurran da suka shafi Najeriya, ya rika karakaina kasashe tamkar mai dillancin jiragen sama, bai sha suka da caccaka da kukan da-na-sani ba, kamar yadda talakawan da suka zabe shi ke yi a cikin wadannan kwanaki bakwai na watan Agusta ba.

Buhari ya shiga cikin mawuyacin halin da ya janyo wa kan sa kakkausar suka, musamman daga bangaren wadanda suka rika wahalar da kan su wajen zaben sa, yayin da a kwanan nan ya kauda kai ya kantara wa talakawa abubuwa uku da ya sosa masu rai sosai.

Na farko dai rufe kan iyakoki da aka yi aka hana shigo da abinci ya kara haifar da masifar tsadar kayan abinci.

Tallafi da lamuni da karfafa noma da aka rika yi, bai kawo sauki da rangwamen kayan abincin da ake nomawa a gida ba. Sai ma tsada da suka kara, wasun su ma kudin su na neman nunkawa.

Cikin watan Yuli Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO), ta fitar da kididdigar cewa akalla mutum milyan 40 a Najeriya ba su da cin yau ko na gobe. Wanda ya samu na yau din ma, to ba shi da na gobe.

Romon-kunne da kuma romon-baka da aka yi wa talakawan Najeriya suka yi fatali da mulkin Goodluck Jonathan, har yau dai talaka bai ga wata sa’ida ba, musamman idan ya yi la’akari da cewa shinkafar da ya ke saye naira 500 a lokacin Jonathan, yanzu naira 1,700 ko 1,600 zai saye ta.

Yayin da masara ke neman ta gagari talaka, babu wata dabara ko farfaganda da za a iya yi masa har a hana shi tuna baya, ya na rokon Ina ma gwamnatin da aka kayar ta dawo!

Karin Kudin Wutar Lantarki:

Ba komai ya bakanta rayukan ‘yan Najeriya ba, sai ganin yadda gwamnati ta cire tausayin talakawa ta kara kudaden a daidai lokacin da ba a murmure daga dukan fasa kwakwalwa da aka yi musu a lokacin barkewar cutar Coronavirus ba.

Karin kudin wutar lantarki bai gama tsinke talakawa da mari ba, sai kuma Buhari ya tura musu karin kudin man ferur. Cikin kwanaki hudu karin kudin wutar lantarki ya zaz-zabga wa ‘yan Najeriya bulalolin da suka gigice. Tun su na ihu har murya ta fara dusashewa, sun koma sambatu.

Hatta wadanda ke raga wa Shugaba Buhari da wadanda su ka ci gaba da hakurin zama cikin mota, su na ta sauka tun kafin a kai inda shugaban ya yi alkawarin kai talakawa. Wasu na cewa direba ya kauce hanya, wasu kuma na cewa a mayar da su tashar da aka dauko su. Wasu kuma cewa suke yi ashe ‘motar Alpha’ suka shiga a rashin-sani.

Irin yadda matsaloli suka dabaibaye Arewa kakaf, daga kisa sai kashewa, sai mutuwa sai macewa. Daga hari sai harbewa, sai garkuwa sai bindigewa, babu wani shugaban da zai kara kudin fetur da kudin wutar lantarki a lokacin da abinci ke kara tsadar bala’i, sannan a ce ba za a ragargaje shi ba.

Share.

game da Author