TSADAR KAYAN ABINCI: Buhari ya ce abin ya na damun sa

0

Shugaba Muhammdu Buhari ya nuna tsananin damuwa da takaici ganin yadda farashin kayan abinci ke ci gaba da yin tashin-gwauron-zabo a ƙasar nan.

Buhari ya ce inda ma abin ya fi ƙara damun sa, shi ne yadda farashin ke ci gaba da tashi a daidai lokacin da tattalin arzikin Najeriya ke tafiyar hawainiya, sakamakon tarnakin da cutar Coronavirus ta yi wa tattalin arzikin Najeriya.

Wannan damuwa ta Shugaba Buhari, ta na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na Fadar Shugaban Ƙasa, Garba Shehu ya fitar a ranar Laraba.

Sanarwar ta fito ne a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke zaman makokin karin kudin wutar lantarki, sannan kuma a ranar da aka bada sanarwar ƙarin kuɗin fetur.

Tuni dai har masu gidajen mai a garuruwa har da Abuja sun fara sayar da lita ɗaya a kan naira 161.

Tun a rranar Laraba bayan NNPC ta yi sanarwar kara wa fetur kudi zuwa 151 farashin sari, sai IPMAN, wato Ƙungiyar Dillalan Fetur Masu Zaman Kan Su, suka fitar da sanarwar cewa sun yanke shawara za su sayar da lita ɗaya a kan N161.

IPMAN ta ce a haka ne kaɗai za su iya cin riba idan suka sayi lita 1 kan Naira 151 daga gwamnati.

Sanarwar ta ce “Shugaba Muhammadu Buhari, ya nuna damuwar gwamnatin sa game da hauhawar farashin kayan abinci a faɗin ƙasar nan a daidai lokacin da tattalin arzikin ƙasar ya ke cikin halin ƙunci sakamakon matsalolin da annobar korona ta jawo a faɗin duniya.

Buhari ya bai wa ƴan Najeriya tabbacin cewa wannan halin ƙunci na tsadar kayan abinci abu ne na dan lokaci, ba mai dorewa ba, inda ya kara da cewa gwamnatin sa ta fara nema tare da kafa matakai na saukaka lamarin.

Tsadar Abinci: Laifin Ƴan Kasuwa Ne -Buhari

Shugaba Buhari ya waiwaya kan ƴan kasuwa, ya zarge da cewa su ne ummul-haha’isin jawo ƙaranci da tashin farashin kayan abinci a kasuwanni.

“Duk da ya ke Allah ya taimake mu an sami isasshen ruwan sama wanda ake tsammanin samun kyakkyawar damina kan kai ga faɗuwar farashin kayan abinci tare da saukaka wa al’umma, damuwar gwamnati a nan ita ce dabi’ar cutarwa a zukatan wasu ƴan kasuwa ta yi matukar ƙaruwa a tsakanin ƴan kasuwa a cikin ƴan shekarun da suka gabata. Hakan ke sa a ga saukin da za a samu ya zama na dan kankanen lokaci.”

Shugaba Buhari ya ce daga cikin matsalolin da aka samu a kakar bana, wadanda suka faru sakamakon bullar annobar cutar Korona da ta shafi duniya baki daya, har da jinkirin da aka samu wajen sayo kayayyakin hadi na samar da takin zamani a gida da kuma mugun halin wasu kamfanonin sarrafa shinkafa, wadanda kan biya kowane nau’in farashi don ganin cewa shinkafar ba ta yanke a kamfanonin su ba.

Buhari ya ce an gano cewa mafi yawan lalatattun dillalan da ke haddasa karancin kayan abinci ta hanyar saye daga hannun manoma sannan su sayar ga jama’a a kan matsanancin farashi, ba ‘yan Najeriya ba ne, ‘yan kasashen waje ne.

“Yanzu haka Shugaban Kasa ya bayar da izinin fitar da kayan abinci daga rumbunan ajiyar kayan abinci na gwamnati, da suka hada da tan 30,000 na masara ga kamfanonin da ke yin abincin dabbobi don saukaka tsadar kiwon kaji.

“Shugaba Buhari ya tattauna wasu daga cikin wadannan al’amurra tare da ƙungiyoyin masu samar da abinci da abin ya shafa, musamman manoman shinkafa da sauran nau’ukan abinci na tsaba.

“Da haɗin kan su, ba da dadewa ba hauhawar farashin kayan abinci zai zama tarihi.”

Share.

game da Author