TATTALIN ARZIKI: Yadda kayan gonar da Najeriya ke shigo da su suka karu, wadanda ta ke fitarwa suka ragu – NBS

0

Adadin kayan gonar da Najeriya ke shigowa da su a kasar nan da kashi 59.1 cikin watannin Afrilu zuwa Yuni, 2020, idan aka kwatanta da adadin watannin farkon shekara, daga Janairu zuwa Maris.

Sannan kuma ya karu zuwa kashi 66.28 idan aka auna da adadin na watannin Afrilu zuwa Yunin shekarar 2019.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin Hukumar Kididdigar Alkaluman Bayanai ta Kasa (NBS).

Bayanin na kunshe a cikin rahoton da NBS ta fitar a kan Ratoton Bayanan Hada-hadar Cinikayya Da Kasashen Waje, a ranar Laraba.

Rahoton ya ci gaba da cewa Najeriya ta yi hada-hadar cinikayyar kayan gona na naira bilyan 493.7.

Sai dai kamar yadda rahoton ya bayyana, Najeriya ta fitar da kayan gona na naira bilyan 78 1 kadai. Duk sauran kudaden cinikin na kayan amfanin gona da aka sayo daga waje ne, aka shigo da su Najeriya.

“Nazarin da rahoton ya fitar ya nuna kayayyakin da aka shigo Najeriya da su Najeriya, an lafto su ne daga Nahiyar Asiya, Turai da Amurka.

NBS ta ce kayan gonar da aka fitar a wadannan watanni uku, sun hada da koko da kashu da wasu kayayyakin amfanin gona din.
Kasashen da aka fitar da mafi yawan kayan gona daga Najeriya, sun hada da Natherland, Indonesiya da Amurka.

An kuma fitar da wasu amfanin gonar zuwa Japan da China. NBS ta ce an fitar kwarorin kashew na naira bilyan 12 zuwa Vietnam, sai kuma ‘durum’ ta dala naira bilyan 41 da aka shigo da ita daga Amurka, Rasha da Latvia.

Har yanzu dai harkokin noma a Najeriya ta tanjan-tanjan kasancewa har yau Najeriya ko isassar masarar da za ta wadaci kasar ba ta iya nomawa.

Kwanan nan Najeriya ta bada sanarwar hana shigo da masara daga waje. Wannan sanarwa ta haifar da hauhawar farashin kayan abincin kaji a Najeriya.

Share.

game da Author