Bari na fara da wata muguwar fata ko addu’a, wadda tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya yi wa Adams Oshiomhole, cikin wata hira da aka yi da shi, a watan Yuli, 2020.
“Ina ji ina gani Adams Oshiomhole don kawai ya na shugabancin jam’iyyar APC, ya rika ci min mutunci da tozarta ni a jaridu da wuraren taruka. To ga shi nan shi ma an cire shi daga shugabancin jam’iyyar. In dai siyasar Najeriya ce, to mu nan lokaci zai zo sai ta dagule wa Oshiomhole, har ya koma ya na tikar rawa tsirara a kasuwa!”
Kayen da Gwamna Godwin Obaseki ya yi wa Ize-Iyamu a zaben Gwamnan Jihar Edo, ko shakka babu sai Adams Oshiomhole ya fi shi jin zafin kayen. Ba don komai ba, saboda shi ne kullin igiyar siyasar sa ya faske.
Shin mukami a gwamnatin tarayya Shugaba Muhammadu Buhari zai ba shi, ko kuwa shi ma watsi za a yi da shi, kamar yadda Buhari ya yi da wanda Oshiomhole ya, gada a shugabancin jam’iyya, wato John Oyegun?
Bai wa Oshiomhole mukami dai wasu na ganin ganganci ne, domin dagula ma’aikatar da za a dora shi zai yi, kamar yadda ya dagula jam’iyyar APC.
Gigitar Da Oshiomhole Ya Jefa Kan Sa:
Bayan ya yi nasara a kotu, an ba shi kujerar gwamnan Edo, cikin Nowamba, 2008, Oshiomhole ya rika dukan kirji cewa, ya kashe siyasar ubangida murus a Najeriya. Saboda ya hana Anthony Anenih da irin su Tom Ikimi yin rawar gaban hantsi a siyasar Edo.
Bayan ya sauka daga gwamna, an nada shi Shugaban APC, cikin 2018, inda ya rika rikici daga sama har kasan jam’iyyar. Hakan ya haifar da asarar jihohi a zaben 2019 da APC ta yi.
Kayar da yaron sa Ize-Iyamu da aka yi, ya kara tabbatar da cewa an kunyata Oshiomhole a siyasar Najeriya.
Shin zai koma ya nemi mukamin Sanata ne? Idan Sanata zai neman, to fa sai ya jira sai 2023, shi ma sai idan wanda ke wakiltar Shiyyar Edo ta Arewa ya nuna rashin muradin sake fitowa takara.
Ko kuwa shugabancin jam’iyya zai sake nema a zaben shugabannin APC mai zuwa cikin karshen wannan shekarar?
Anya Gwamnonin APC za su sake amincewa su damka shugabancin jam’iyyar a hannun mutumin da ya yi mata rikon sakainar kashin da ta yi asarar jihohi, cikin har da jihar sa ta haihuwa, wato Edo.
Discussion about this post