Shugaban Amurka Donald Trump ya yi ikirarin cewa dan takarar shugaban Amurka na jam’iyyar Democrat, Joe Biden rikakken dan kwaya ne.
Trump ya bayyana haka a wata tattaunawa ts musamman da kafar yada labarai ta Fox News ta yi da shi.
Ranar Asabar din nan ce Fox News za ta buga tattaunawar, wadda suka yi da Trump, gaba dayan ta.
Yayin da zaben shugaban kasar Amurka ke karatowa, takara na ci gaba da kara zafi a bangarorin jam’iyyun biyu na Amurka, wato Republican ta su Trump, sai kuma Democrat ta su Joe Biden.
Yayin da kowane bangare ke kallon shi zai yi nasara, cacar-baki ta kazamce tsakarin Trump da Biden, har ta kai ya kira Biden dan kwaya.
“Ji na yi ana cewa kafin Biden ya hau duro ya yi kamfen, sai ya nuske da kwayar ‘a-ji-garau tukunna, sannan ya ke yin jawabi a bainar jama’a.”
Trump mai shekaru 74 a duniya, ya sha kokarin ya nuna cewa kwakwalwar Biden ba ta da saiti.
Ya kara da cewa shi bai damu ba don hargitsi ya barke a ranar zabe.
“Babu komai don hargitsi ya barke a ranar zabe. Domin cikin gaggawa za mu tarwatsa gungun masu hargitsin.” Cewar Trump.
Trump na fama da matsalar zargin sakacin da ake yi masa yadda ya bari dubban Amurkawa su ka mutu sanadiyyar Annobar Korona.
Shi kuma Biden ana jin tsoron sa, domin shi da babbar ‘yar kamfen din sa, Hillary Clinton, duk akidar kai wa kasashe hari gare su. Su na da halayyar son ganin Amurka ta yi kane-kane a duniya, ta hanyar kai wa kasashe hare-hare.