Ƴan Najeriya sun shiga soshiyal midiya sun ragargaji Shugaba Muhammadu Buhari, saboda ya bai wa Gwamna Abdullahi Ganduje Jirgin Shugaban Ƙasa, ya lula kamfen din APC a jihar Edo.
Ganduje shi ne Shugaban Kwamitin Kamfen din APC a zaɓen gwamnan jihar Edo da za a yi ranar Asabar, 19 Ga Satumba.
Ganduje ya tafi kamfen ɗin a cikin jirgin tare da jami’an jam’iyyar APC a ranar Asabar.
Daga cikin su akwai Shugaban APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas, Shugaban Masu Rinjaye, Ado Doguwa, da Sanata Barau Jibrin na Kano.
Abdulallahi Abbas dai shi ne Shugaban APC na Kano, wanda aka nuno wani bidiyon sa, a kusa da ranar zaben gwamna na 2019 a Kano, inda ya tara ‘yan jagaliya ya na cewa, ko PDP ta ci zabe, ba za su ba ta ba.
Cikin 2019 an soki Buhari saboda ya bar ƴar sa Hanan ta dauki jirgin Shugaban Kasa ta je ziyarar yawon buɗe-idon nazari a Jihar Bauchi.
“Ai wata al’ada ce Buhari ya tsira kuma ya ke ci gaba da ita, wato al’adar mulkin kama-karya da rashin ganin darajar ‘yan Najeriya.” Haka Inibehe Effiong ya shaida wa PREMIUM TIMES.
Ya ce, “karya ka’idar aikin Ofishin Shugaban Kasa ne a dauki Jirgin Shugaban Kasa a rika bai wa abokai da ‘yan jam’iyya su na gallafiri a cikin sa a kasar nan.”
“Sashe na 100 na Dokokin Zabe, wanda aka yi wa kwaskwarima cikin 2010, ya haramta yin amfani da kayan gwamnati zuwa wurin kamfen da su.” Inji Effiong.
“Gwamnan Kano ba Shugaban Kasa ba ne, kuma ba ma’aikacin da ke aiki a karkashin shugaban kasa ba ne.”
Shi ma dan taratsin kare hakkin jama’a, wanda aka taba tsarewa a kukrkukun Kano, Deji Adeyanju, ya yi Allah-wadai da abin, ya ce, “facaka da kudi ce kawai da kuma zubar da kimar Ofishin Shugaban Kasa.”
Shi ma Shugaban Ƙungiyar Gangamin Yaki da Rashawa (Network Against Curruption), Olarenwaju Suraj, ya yi tir da yadda ake daukar jirgin Shugaban Kasa ana bai wa jama’a su na gallafiri da shi.
Discussion about this post