Shekarau, Barkiya, Sanatoci 10 da basu taba gabatar da Kudiri a majalisa ba

0

Duk da cewa wasu da dama cikin sanatocin dake majalisar dattawa sun gabatar da kudirori sama da 10 zuwa yanzu, har yanzu shugaban Majalisar Ahmed Lawan da Sanata Ibrahim Shekarau da wasu sanatoci basu taba gabatar da koda kudiri daya bane har yanzu a wannan zango na majalisa.

Ba kamar yadda takwaransa na majalisar Tarayya ba, Kakakin majalisa Femi Gbajabiamila, shi ko zuwa yanzu ya gabatar da kudirori har 15 tun daga ranar da aka rantsar da su a shekarar bara.

Sanata Ibrahim Shekarau daga Jihar Kano da Sanata Barkiya daga jihar Katsina da wasu basu taba gabatar da kudiri a majalisar ba kamar yadda wasu sanatocin sai dumama kujerun majalisa suke yi har yanzu basu gabatar da koda kudiri daya tal ne a zauren majalisar.

Wadannan sanatoci sun hada da, Godiya Akwashiki, Emmanuel Oker-Jev, Adamu Bulkachuwa, Peter Nwaoboshi da Chris Ekpenyong. Sauran sun hada da Kabir Barkiya, Ibrahim Shekarau, Nicholas Tofowomo da Lawali Hassan.

Ko da yake kundin tsarin mulkin kasa bai tilasta sai dole dan majalisa ya gabatar da kudiri a majalisa ba wasu da dama na ganin baya ga gabatar da kudiri akwai wasu ayyukan da dan majalisa zai rika yi.

Sanata Sani Musa daga jihar Neja ne ya fi duka sanatocin Arewa yawan wanda ya fi gabatar da kudiri a zauren majalisa.
Ya mika akalla kudirori 13 sai Ali Ndume daga Jihar Barno dake da Kudiri 12.

Sanata Istifanus Gyang ya gabatar da kudiri 11 a zauren majalisa.

Sanata Stella Oduah ce ta fi kowane sanata yawan kudirori da ta gabatar a domin zama doka a zauren majalisar.

Sauran sanata sun hada da Ovie Omo-Agege – 20, Uche Ekwunife – 17, Ifeanyi Ubah – 13, Gershom Bassey – 11, Adeola Olamilekan – 10, Bamidele Opeyemi – 10 sai tsohon mataimaki shugaban majalisar Ike Ekweremadu, 10.

Share.

game da Author