Gwamnatin jihar Kaduna ta gargadi mutane su daina yada jita-jita da labaran karya kan nadin sabon sarki da ake jira
Kakakin fadar gwamnati Kaduna, Muyiwa Adekeye ya sanar da haka a Kaduna.
Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ziyarci garin Zazzau, domin halartar addu’o’in kwana uku da aka yi a fadar sarkin Zazzau.
Cikin wadanda suka raka gwamnan sun hada da gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi, Gwamnan Neja, Abubakar Sani, Gwamnan Filato Simon Lalong da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.
Bayan addu’o’i da aka gudanar, fadar gwamnatin Kaduna ta gargadi masu yada jita-jita da su daina haka cewa har yanzu masu zaban sarki suna tattar sunayen wadanda za su turo wa gwamna El-Rufai domin zaban daya daga ciki.
Tun bayan rasuwar Sarkin Zazzau marigayi Shehu Idris, ya’yan sarakunan gidajen sarautar Zazzau suka fantsama neman zama sarkin kasar Zazzau.
Wadanda ke a kan gaba cikin masu neman sun hada da Yeriman Zazzau Mannir Jaafaru, Ahmed Magajin Garin Zazzau, Aminu Idris, Turakin Zazzau sai kuma Iyan Zazzau, Bashar Aminu.
Yerima Mannir a na zaton zai samu daurin gindin shugaban Kasa Muhammadu Buhari ganin irin kusanci na kud-da-kud da ke tsakanin su. Shi kuma Ahmadu magajin Gari na da kusanci na jini da iyayen sa wanda shima yana kan gaba wajen neman sarautar Zazzau din.
Gwamnati ta ce da zaran an mika mata sunaye za ta yi abinda ya dace. Tana mai cewa kowa ya natsu a jira wadanda hakkin nadin sarkin ke hannun su su gama aiki a kai.