Kakakin ma’aikatar tsaron kasa John Enenche yayi kira ga mazauna garin Abuja da su kwantar da hankalin su cewa ana yin binciken zargin da ya karade gari cewa wai Boko Haram zasu dira Abuja domin afkawa mutane garin.
An dai samu wata takardar sirri da ta bayyana daga ofishin hukumar Kwastan ta Ƙasa inda ta ke gargaɗin mutane cewa an samu rahoton Boko Haram na kakkafa wasu sansanoni a dazukan dake kewaye da Abuje domin shirin afkawa babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja da jihohin Nasarawa da Kogi.
PREMIUM TIMES ta nemi ji daga hukumar Kwastan domin samun ƙarin bayani a akai amma Kakakin hukumar ya shaida cewa bai san da wannan magana ba kuma bashi da masaniya game da irin wannan takarda da ke ƙunshe da saƙon haka daga wannan hukuma.
Takardar ta ƙunshi wasu wurare da aka ce wai Boko Haram na kafa sansanoni kamar haka; Dajin Kunyam dake titin zuwa filin jirgin saman Abuja, kusa da rukunin gidaje na DIA; Dajin Robochi dake Gwagwalada; dajin Kwaku dake Kuje, Abuja; Dajin Unaisha dake karamar hukumar Toto jihar Nasarawa da Dajin garin Gegu dake kusa Idu town jihar Kogi domin shirin afkawa Abuja.
Tun bayan jin wannan sanarwa, mutanen Abuja kuma ciki ya duri ruwa.
Sai dai kuma ma’aikatar tsaro ta yi kira da roƙon mutane su kwantar da hankalin su, cewa lallai jami’an tsaron Najeriya a tsaye suke domin samar da tsaro ga mutane baki daya.
Discussion about this post