Shugaba Muhammdu Buhari ya yi kira ga al’ummar jihar Kaduna su haɗa kai, su zama ƴan uwan juna domin tilas sai an yi hakan sannan ci gaba zai wanzu a fadin kasar.
Buhari ya ce sai da zaman lafiya sannan yakwar arziki da ci gaban jama’a ke ɗorewa.
“Kashe-kashe da lalata dukiyoyi da kadarori ba ya haifar da komai sai zaman gaba da maida al’umma koma koma-baya.”
Buhari ya yi wannan kira a cikin jawabin sa na buɗe Taron Bunƙasa Tattalin Arzikin Jihar Kaduna, na 5, wato Kaduna Economic and Investment Summit, KADInvest.
Ya yi bayanin ne a ofis, inda aka nuna shi ta talbijin din Zoom ya na bayani.
Ya ce KADInvest ya yi nasara sosai, tun bayan fara taron cikin 2016. Ya ce Jihar Kaduna ta cancanci jinjina, domin shekaru biyar kenan a jere duk shekara ba a fasa shirya taron ba.
“Shirin ya kawo ci gaba da bunƙasa Jihar Kaduna ta hanyar samun masu zuba jari a jIhar, samar da ayyukan yi ga matasa da kuma kara samar da kuɗaɗen shiga ga gwamnatin jiha.” Inji Buhari.
“Nan na zo cikin 2017 na buɗe katafaren masana’antar abincin kaji da kuma wurin kiwon kajin a Olam Farm.
“Ci gaba ta ɓangaren hasken lartarki a karkashin Blue Camel, kiwon kaji da gina gonakin kiwon kaji daban-daban da bunƙasa sarrafa ƙarafa, duk ayyukan ci gaban da aka samu ne bayan fara KADInvest a Kaduna.”
Buhari ya roƙi al’ummar jihar su zauna lafiya da juna domin su ci gaba da bunƙasa Jihar fiye ma da yadda ake ta hanƙoron haɓɓaka ta a yanzu.