RIJIYA GABA DUBU: Matatun mai biyu na Najeriya sun ci naira biliyan 85.9 a wata 13, amma ba su tace ko litar mai ɗaya ba

0

Matatun mai uku na Najeriya sun lashe naira bilyan 148 a cikin watanni 13, amma man da aka tace bai kai metirik tan 40,000 ba.

Wani bayani da NNPC ta fitar a cikin watan Yuni ya tabbatar da haka.

Amma duk da haka NNPC ya tsaya kare kan sa cewa an samu karancin tace danyen man ne saboda gyare-gyaren matatun da ake kan yi.

Su dai wadannan matatu guda uku, su na da karfin tace danyen mai har ganga 445,000 a kowace rana gaba dayan su.

Matatar Fatakwal na iya tace ganga 210,000 a kowace rana. Ta Kaduna kuma ganga 10,000 kacal a rana, sai kuma ta Warri ganga 125,000 a kowace rana.

Amma tun daga watan Yuni 2019 har zuwa Yuni 2020, matatun su uku abin da suka tace bai wuce metrik tan 38, 977 na danyen man fetur ba.

A matatar Kaduna da an samu gibi na naira bilyan 62 a cikin watanni 13. Haka dai PREMIUM TIMES ta binciko, a nazarin da ta yi wa rahoton na NNPC dalla-dalla.

Matatar Warri ba ta tace ko cikin kofi daya ba, amma lashe naira bilyan 42.1, kuma ta sake tashe wasu naira bilyan 43.8 daga aljihun gwamnati.

Ita ma matatar NNPC ta Kaduna da tace kalilan din da aka dibga asara, tun a watan Yuli, 2019 ta yi tacewar. Daga nan har yau ba ta sake tace ko kwalba daya ‘yar-cigila ba.

Cikin watan Yuni na 2020, gwamnatin Buhari ta kashe matatun naira bilyan 10.23, duk da cewa zaman-dirshan kawai ma’aikatan hukumar ke yi a Kaduna.

Duk da NNPC ta ce gyara ake yi, shi ne dalili, rahoton binciken-kwakwaf da aka gudanar, ya nuna cewa an dibga asarar naira tiriliyan1.64 daga 2014 zuwa 2018.

Matatun Fatakwal da na Kaduna sun yi asarar naira bilyan 208.6 cikin 2015. Cikin 2015 sun yi asarar naira bilyan 252.8. Cikin 2016 asarar naira bilyan 299.6. A 2017 asarar naira bilyan 412. A 2018 kuwa naira bilyan 475.

Masu sukar NNPC da satar da suka ce ana dibgawa a hukumar, sun nemi a saida NNPC din a hannun ‘yan kasuwa, su rika tace mai su na bai wa Najeriya na kason.

Haka Atiku Abubakar ya bayyana cewa zai yi idan ya ci zaben 2029.

Sukar da ‘yan Arewa su ka rika yi masa, ba ta yi tasiri ba, domin an fi dibga asara a NNPC lokacin mulkin Buhari.

Share.

game da Author